Ba ni da kawa ko daya a farfajiyar Kannywood – Halima Ibrahim
Za mu fara da tarihinki, shin wace ce Halima? Sunana Halima Ibrahim Yusuf. An haife ni a Kano, na yi makarantar firamare a Gold Star Primary School, sannan na yi sakandare a Liberty College, kafin in wuce zuwa Jami’ar Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola, inda na karanta Ilimin Kimiyyar Kwanfuta (Computer Science). Me […]

Za mu fara da tarihinki, shin wace ce Halima?
Sunana Halima Ibrahim Yusuf. An haife ni a Kano, na yi makarantar firamare a Gold Star Primary School, sannan na yi sakandare a Liberty College, kafin in wuce zuwa Jami’ar Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yola, inda na karanta Ilimin Kimiyyar Kwanfuta (Computer Science).
Me ya ja hankalinki har kika shiga harkar fim?
Abu ne da na dade ina so, amma ban taba nunawa a fili ko in nuna a gidanmu cewa ina so ba, sai da na bari na kammala jami’a tukunna, kafin in tambaya a gidanmu. A lokacin na ce idan an bar ni sai in yi, idan kuma ban samu izini ba sai in hakura, amma dai zan ci gaba da kaunar fina-finai da kuma ’yan fim. Cikin ikon Allah kuwa aka bar ni a gida.
Wadanne fina-finai ne suka taka rawa wajen jan hankalinki har kika shiga harkar fim?
Gaskiya fina-finan suna da yawa, fina-finan da na kalla suka ba ni sha’awa, suka kuma ja ra’ayina suna da yawa gaskiya, ban ma san wanne ne zan fara gaya maka ba. Misali, daga ciki akwai ‘Jinin Jikina’ wanda Abdul M. Shareef da Rahama Sadau suka yi, akwai ‘dan Marayan Zaki’ wanda Sadik Sani Sadik da Nafisa Abdullahi suka yi, fina-finan suna da yawa.
Lokacin da kika yanke shawarar za ki shiga harkar fim, shin ta wacce hanya kika bi?
Akwai kanwar mahaifiyata mai suna Asma’u Musa, wadda ta yi fim a baya kafin ta yi aure ta daina. To, ta hanyarta na shiga, a lokacin da na fada a gida cewa ina so in yi fim, sai ta sa mini baki, ta yi wa iyayena cikakke kuma gamsasshen bayani a kan harkar, sai aka bar ni.
Zuwa yanzu kin yi fina-finai kamar nawa?
Na yi fina-finai kamar 20, fina-finan sun hada da ‘Uwar Bari’ da ‘Rabu Da Maza’ da ‘Manakisa’ da ‘Cellphone’ da Lafiya’ da Leka Gidan Kowa’ da ‘Halin Mutum’ da ‘Ja Muje’ da ‘Farin Jakada’ da ‘Zinariya’ da ‘Bakon Al’amari da ‘Wani Buri’ da sauransu.
A cikin fina-finan da kika yi wanne ne ya fi burge ki?
Gaskiya wanda ya fi burge ni shi ne ‘Uwar Bari’ wanda kamfanin Iyantama Multimedia ya shirya, Hafizu Bello ya ba da umarni. A cikin fim din ni ce babbar jaruma, inda na fito a matar jarumi Sadik Sani Sadik, inda ya rika yi mini abubuwan da ba su dace ba. Ni kuma na rika hakuri, fim din yana nuna abin da yake faruwa a cikin al’umma ne, sannan ya yi hannunka mai sanda ga masu aikata haka.
Yaya alakarki take da saura masu shirya fim?
Ina da kyakkayawar alaka da ’yan fim, ina son zaman lafiya, ba na son rigima, don haka ina zama da kowa lafiya, idan abu ya kai ni wuri, zan yi ne sannan in bar wurin, ba zan tsaya a yi ta cece-kuce da ni ba. A zahirin gaskiya ma ba ni da wata kawa a Kannywood.
Wadanne matsaloli kika fuskanta a harkar fim?
A gaskiya ban fuskanci kowace matsala ba, walau a Kannywood ko a gida. Komai zan yi sai na nemi shawara, domin ba na yin abu kai tsaye.
Zuwa yanzu wacce nasara kika samu a harkar fim?
Na samu nasarori sosai, musamman ma irin rawar da na taka, da na fito a cikin fim din ‘Uwar Bari.’ Fim ne da nake alfahari da shi sosai, a wurina hakan babbar nasara ce.
Mene ne bambancin da ke akwai tsakanin lokacin da ba ki fara fim ba da kuma yanzu da kika kasance babbar jaruma?
Akwai bambanci sosai. A da ba a san fuskata ba, don haka zan iya yin komai ba tare da wani ya lura da ni ba, amma a yanzu ba haka ba ne, duk inda aka gan ni sai mutane su taru, sannan yanayin da nake sanya sutura ya sauya. Idan da zan iya fita yadda na ga dama, yanzu ba zai yiwu ba. A da zan iya shiga kasuwa in yi cefane yadda nake so, amma yanzu hakan ba zai yiwu ba.
Wadanne darussa kika karu da su sakamakon shiga Kannywood?
Na karu da darussan cewa idan na kama kaina a matsayina na mace zan zauna lafiya da mutane. A da ina tunanin rayuwar jami’a tana da wahala, amma a yanzu sai na tabbatar da ta masana’antar fim ta fi wahala, saboda na hadu da mutane daban-daban wadanda suke da halaye daban-daban. Na koyi hakuri kasancewar da ba a yi mini in kyale, amma yanzu ba haka ba ne, mutum zai iya yi mini abu sai in kalle shi kawai. Na kara koyon iya mu’amala da mutane, sannan na koyi iya shiga cikin mutane. Na koyi darasin kasancewa mai bincike kafin yanke hukunci, sannan fina-finan da na fito sun kara mini ilimi wajen zaman duniya da kuma na aure.
Ta bangaren abinci fa wanne kika fi so?
Na fi son abincin da mahaifiyata ta dafa, babu abincin da ya kai mini nata dadi da gamsarwa. Kowane abinci na samu a wani wuri, duk kudin da aka kashe masa, ni dai ba ya kai na mahaifiyata dadi. Amma dai na fi son ta yi mini tuwon shinkafa da miyar yakuwa, ko tuwon shinkafa da miyar kubewa.
Wane launi kika fi so?
Ina son launin kasa, ka ga launi ne da ba ya jan hankalin mutune kamar ruwan dorawa da ja da sauransu.
A bangaren abin hawa fa?
Ina tsananin son Mercedez Benz.