Ba ni da ko Dala daya a kasar waje – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako (mai ritaya) wanda ya dawo Najeriya daga gudun hijirar da ya yi a bara, ya ce bai mallaki ko da Dala daya ba a wata kasa daga cikin kasashen duniya. Gwamna Nyako ya kuma kalubalanci dukkan masu zarginsa da tu’annati da kudaden gwamnati su kawo shaidar da za […]

Ba ni da ko Dala daya a kasar waje – Nyako
Ba ni da ko Dala daya a kasar waje – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako (mai ritaya) wanda ya dawo Najeriya daga gudun hijirar da ya yi a bara, ya ce bai mallaki ko da Dala daya ba a wata kasa daga cikin kasashen duniya.

Gwamna Nyako ya kuma kalubalanci dukkan masu zarginsa da tu’annati da kudaden gwamnati su kawo shaidar da za ta nuna haka.
Tsohon Gwamnan ya sake musanta rahotannin da suke cewa ya gudu daga Najeriya ne, saboda neman da Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ke yi masa, inda ya ce barazanar kisa da ake yi masa ce ta sa shi yin hijira daga kasar nan.
Admiral Nyako ya ce ya je Hukumar EFCC ne domin jin dalilin neman da suke yi masa, inda suka sallame shi cewa za su sake nemansa a nan gaba.
Admiral Nyako dai ya bar Najeriya ne jim kadan da tsige shi daga kujerar Gwamnan Jihar Adamawa, a daidai lokacin da yake takun-saka da fadar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, bayan da ya zargi Jonathan din da hannun a matsalar Boko Haram da ta addabi jihohin Arewa maso Gabas, musamman Borno da Yobe da Adamawa, inda ya yi zargin cewa Boko Haram wani shiri ne na wargaza Arewa da karya tattalin arzikinta.