Ba ni da matsalar siyasa da Gwamnan Bauchi – Sanata Hamma Misau

Sanata mu fara duba batun rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, inda aka yi ta samun kungiyoyi da daidaiku wadanda suka yi zanga-zangar nuna cewa ya dawo ko ya yi murabus. Koda yake majalisa kun fidda sanarwa cewa zamansa a Landan bai saba ka’ida ba, shin a dunkule me zaka ce game da dawowar tasa a […]

Ba ni da matsalar siyasa da Gwamnan Bauchi – Sanata Hamma Misau

Sanata mu fara duba batun rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, inda aka yi ta samun kungiyoyi da daidaiku wadanda suka yi zanga-zangar nuna cewa ya dawo ko ya yi murabus. Koda yake majalisa kun fidda sanarwa cewa zamansa a Landan bai saba ka’ida ba, shin a dunkule me zaka ce game da dawowar tasa a yau?

To da farko dai mun gode wa Allah da Ya bas hi sauki ya dawo don cigaba da ayyukansa na shugabancin kasa. Sannan abu na biyu shi ne sha’anin ‘yan Najeriya yana ba ni mamaki ainun, kuma al’umma ce dake bin addinai ko dai musulmi ko kirista, inda aka nuna cewa rayuwa da mutuwa da mulki duka na Allah ne, amma sai ka rika ganin sabanin hakan. To wannan yana nuna cewa ba mu fahimci addinin ba ne ko kuwa? Yanzu su wadannan da suka yi zanga-zangar cewa Buhari ya dawo ko ya sauka, da me suka dogara suke wannan fafutika? Da addinin ko da kundin tsarin mulki? Ka ga kamata ya yi ace dukkan al’ummar Najeriya sun dukufa da yi masa addu’ar samun sauki a matsayinsa na shugabanmu, saboda shi Allah Ya baiwa jagorancin, sai kuma Allah Ya jarrabe shi, anan ko kadan ma ba sauka ya kamata ace muna neman ya yi ba, addu’a zamu masa Allah Ya ba shi lafiya. 

Sannan na biyu kuma shi ne tsarin mulkin kasar, mu dai a majalisun nan biyu mun yi ittifakin cewa Shugaba Buhari bai saba ka’ida ba! Abu biyu kawai ake nema ya yi, kuma ya yi su duka, na farko shi ne ya rubuta ya sanar da majalisun nan cewa zai tafi jinya, na biyu kuma idan lamarin zai dauki lokaci, to ya baiwa mataimakinsa damar yin ayyukansa na shugabanci. To wanne ne bai yi ba. Saboda haka a lokacin da muka ga an maida lamarin na siyasa ana ta zanga-zanga, muka fitar da sanarwa cewa Buhari bai saba ka’ida ba, kuma akan sa muke har zuwa yau da Allah Ya dawo da shi. Kuma na taba fadi kwanakin baya a gidan Rediyon Muryar Amurka cewa koda shekaru biyun duka ya yi babu wani hakki akansa.

Majalisa ta gabatar da wani kuduri na baiwa matasa damar tsayawa takarar kowace kujerar shugabancin siyasa, a matsayinka na matashi ya ka kalli fa’idar wannan kuduri ga matasan kasar nan?

To hakika wannan kuduri ne mai kyau, kuma yana daga cikin manyan kudurorin da majalisa ta cimma a wannan karon. Saboda idan ba hakan ka yi ba, matasanmu ba za su samu damar shiga a dama da su ba. Sannan mun kalli fa’idar ganin ana samun sababbin jini a harkar mulki, domin kowa da irin rawar da zai taka wajen tafiyar da kasa. Idan ka kalli shugabannin baya, yawaicinsu sun shugabanci kasar nan ne a kananan shekaru daga 30 zuwa 40, haka gwamnoni da ministoci da dama, kuma an samu nagartaccen shugabancin da ake bukata. Alfanun samun matasan na da yawa wadanda muka kalla, sannan muka amince da wannan kuduri don kawo daidaito a fagen siyasa da shugabanci a Najeriya. Ta yadda kowane bangare ba zai ji cewa ba a kyauta masa ba.

Ya ya kake kallon yawan jam’iyyun da a kullum Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ke kara samarwa a Najeriya, wannan ma duk a cikin fa’idojin takarar matasan ne ko kuwa?

Wato ita hukumar zabe ta na da hurumin bada rajistar sababbin jam’iyyu kamar yadda dokar kasar da ta kafa ta ta ba ta. Amma wasu masana ne ke ganin za a iya samun matsala idan jam’iyyun siyasa suka yi yawa, amma INEC na da hakki ta yi haka nan, wasu ‘yan siyasa na ganin idan jam’iyyu suka yi yawa siyasar ma ba zata yi dadi ba, wasu kuma na ganin idan suka yi yawan za su samu damar tsayawa takara, ka ga ashe har yanzu ra’ayoyin jama’a ake kallo wajen kwace rajistar wata jam’iyya ko baiwa wata. Har ma ana ganin za a iya bada damar yin takara ko da babu jam’iyya. Sannan ita hukumar zabe ta na ayyuka ne gwargwadon dokokin da suka kafata, idan har wata jama’a ta cika sharuddan zama jam’iyya ya zaka yi dole babu zabi sai dai ka ba su, domin za su iya zuwa kotu su nemi hakkinsu, sai dai idan majalisa ce za ta yi doka ta iyakance adadin jam’iyyun da za a samar a kasa irin Najeriya, kuma bana jin za a yi hakan. 

Akwai rahotannin da suke nuna cewa dangantaka ta yim tsami tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi da kuma ku ‘yan majalisar tarayya daga Bauchi. Shin kawo yanzu an dinke wannan baraka ko dai da sauran rina a kaba?

To wannan matsala dai kusan ‘yan jarida ne suka maida ita gagara badau! Idan abu guda ya faru sai ‘yan jarida su shiga su maida shi tamkar goma ne suka faru. To Alhamdulillah ina tabbatar maka cewa idan ma har akwai matsalar, to tana gyaruwa ba kamar yadda kullum ake ruwaitowa a kafafen labarai ba. Kuma insha Allahu ina da tabbacin idan ma har akwai sauran matsalar, to kafin lokacin zabe komai zai daidaita.  

Ranka ya dade wannan na nuna cewa kai baka da wata matsala da Gwamna MA Abubakar a siyasance?

Ni ba ni da wata matsala da shi! Saboda ni ina majalisar tarayya shi yana gwamnan jihar Bauchi, kuma ayyukanmu a bisa doka kowa da nasa, ayyukansa daban nawa daban, sai dai saboda kasancewar muna jam’iyya daya ne, za a iya cewa muna bukatar juna don tafiyar da ayyukan jama’a a jam’iyyance. Don haka ni babu abinda gwamna ya yi mani na batanci, ya na gudanar da ayyukansa a yankina kuma mutane na suna sonsa.

Akwai masu kiraye-kirayen cewa azo a sake fasalin kasar nan saboda tsarin da ake kai a cewarsu ba mai kai kasar ga gaci ba ne. Ya kake kallon wannan dambarwa?

Idan har shugabanni ne me yasa ba su gyara ba a lokacinsu sai da wani ya zo tukun suka gane cewa kasar ba daidai take ba? Gaskiya ina ganin babu wani abu da kasar nan ke bukata face gyaran zuciyoyinmu kawai, idan ka canja fasalin kasar za ka canja fasalin zukatan ‘yan Najeriya ne? Matsalar daga gare mu take ba daga kasar ba, su waye kasar? Ni ina ganin wannan wata yaudara ce kawai da wasu suka shirya, yanzun nan fa wasu suka cimma burinsu ta hanyar zuga mutane cewa su fito su yi zanga-zangar Buhari ya sauka, talakawa kuma ana ta wasa da hankulansu kullum sun kasa ganewa. Yanzu misali idan ka yi dokar ‘yan sandan jihohi, masalaha ce ka kawo ko baraka? Duk sadda ka maida ‘yan sanda hannun gwamna, to lallai sai an gallazawa wadanda kila ba ‘yan jam’iyyarsa ba, sai an uzura wa wadansu, a hakan ma ya muka kare ballantana ka yi wannan. Misali dubi abubuwan da suke faruwa a Taraba da wadansu jihohin ka gani, idan ka yi ‘yan sandan jiha karkashin gwamna me zai faru kenan? Don haka gyaran dabi’a muke bukata ba gyaran fasalin kasa ba. Amma duk mai yin wannan kira saboda siyasa ne kawai ko don burin ya burge wani bangare kawai, amma ba maslaha ba.

A karshe me zaka ce game da yadda Jam’iyyar PDP ke samun karfi ta na ta gunadar ta taruka, inda take hankoran sake kwace mulki hannun APC a 2019?

Wannan dodorido ne kawai! Amma ban ga alamar talakan Najeriya zai sake zabar PDP ba. Duk wanda ka ji yana maganar PDP to dama an yi ta cuwa-cuwa da shi ne a baya kuma ya ji dadin hakan, amma ba maganar kishin kasa ba. Kuma meye sabo a cikin jam’iyyar har yanzu? Idan ka duba zaka ka cewa wadanda suka lalata kasar ne har yanzu a cikinta. Saboda haka wane mai son cigaban Najeriya ne zai kara sanya kuri’arsa a PDP kuma? Musamman mu al’ummar da muka fito daga Arewa maso Gabas, domin a lokacin da ake mulkin PDP barci ma mutum baya iya yi a wannan yankin da ma wasu sassan kasar nan, ba ka iya zuwa garinku baka iya zuwa ko’ina, amma yau Alhamdulillahi da zuwan APC duk an fara mance wadancan wahalhalu na rashin tsaro da tashe-tashen hankula wadda suke haddasa mutuwar jama’a kullu yaumin. Domin abinda zan ce anan shi ne idan maye ya manta, to uwar ‘ya ba ta manta ba. 

Wannan ya tuna min Hukumar sake gina Arewa maso Gabas da rashin tsaro ya haddasa, ina batun ya kwana a majalisa?

Batun hukumar na nan daram bab fashi. Mu a majalisa mun yi duk abinda ya dace kuma gwamnatin tarayya ta amince da batun, domin da zarar shugaban kasa ya sa hannu shike nan, mu a majalisun nan biyu muna gab da gama dukkan gyare-gyaren da zamu karasa don mika wa ga bangaren zartarwa. Kuma da izinin Allah wannan hukuma za ta tabbata kamar yadda aka kirkiro hukumar Neja-Delta kuma al’ummar yankin ke cin wannan gajiya har zuwa yau.