Ba ni da niyyar sake mayar da birnin tarayya zuwa Legas idan na ci zabe —Tinubu
Ya ce ‘yan adawa ne kawai suke yada karyar
Dan takatarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya karyata labarin da ake yadawa cewa zai sake mayar da babban birnin Najeriya zuwa Legas muddin ya zama Shugaban Kasa a 2023.
Tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ne dai ya mayar da babban birnin kasar zuwa Abuja daga Legas a watan Disamban shekarar 1991.
- ‘Har yanzu aniyar Buhari ta cire ’yan Najeriya 100m daga kangin talauci tana nan daram’
- APC za ta kaddamar da manhajar neman tallafin kudi daga ’yan Najeriya
To sai dai a ’yan kwanakin nan, an sami wasu labarai da ke cewa tsohon Gwamnan na Jihar Legas zai sake mayar da babban birnin zuwa jiharsa, idan ya zama Shugaban Najeriya.
Amma a cewar wata sanarwa da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC ya fitar a madadin Tinubun ranar Talata, ya nesanta kansa daga maganar.
“Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC na gargadin ’yan Najeriya kan wani sabon salon yakin neman zabe da aka fito da shi a kan dan takararmu, Bola Tinubu.
“Bayan sun gama karar da dukkan makaman yakin da suka tanada, PDP da LP sun koma yada yarfe da karairayi kan dan takararmu, a kokarinsu na ganin biyan bukatar kashin kansu ko ta halin kaka.
“A daya daga cikin irin wadannan karairayin ne muka ji suna cewa idan Tinubu ya ci zabe a 2023, zai dauke Babban Birnin Tarayya daga Abuja ya mayar da shi Legas. Wannan karya ce tsagwaronta, kuma bayanai sun nuna wasu wadanda PDP ta dauki hayarsu ne suka yada ta, domin cim ma manufarsu.
“Haka ma suka yi ta jirkita maganar cefanar da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), inda suka ce an sayar da shi ne, kamar yadda dan takararsu yake kokarin yi.
“Sai dai sabanin Atiku, Tinubu ba shi da niyyar sayar da NNPC ga ’yan uwa da abokan arziki,” kamar yadda sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Kakakin kwamitin, Bayo Onanuga ya fitar.