Ba ni da niyyar tilasta wa wani shiga Musulunci – Buhari

Dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya gana da Limaman Cocin Katolika na Najeriya inda ya sake nanata kudirinsa na kare matsayin Najeriya na kasa mai bin addinai da yawa tare da barin kowa ya gudanar da addinin da ya zaba.Da yake magana da wakilan Majalisar Bishop-Bishop din Cocin Katolika […]

Ba ni da niyyar tilasta wa wani shiga Musulunci – Buhari
Ba ni da niyyar tilasta wa wani shiga Musulunci – Buhari

Dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya gana da Limaman Cocin Katolika na Najeriya inda ya sake nanata kudirinsa na kare matsayin Najeriya na kasa mai bin addinai da yawa tare da barin kowa ya gudanar da addinin da ya zaba.
Da yake magana da wakilan Majalisar Bishop-Bishop din Cocin Katolika ta Najeriya a Abuja, Janar Buhari ya ce duk da an rika yi masa kazafi da yarfe, ba ya da wata boyayyar manufa ta fifita wani addini, kuma ba zai goyi bayan duk wani yunkuri da wani ko rukunin mutane za su yi don musuluntar ko kiristar da Najeriya ba.
A jawabinsa mai taken: “kasa daya da ta ginu kan ’yanci, zaman lafiya hadin kai da soyayya,” Janar Buhari wanda mataimakinsa Yemi Osinbajo da Daraktan Kamfe dinsa Gwamna Rotimi Amaechi da wasu ’yan kwamitin kamfe da ’yan jam’iyyarsa suka rufa wa baya, ya ce “Ba zai lamunci kowane yunkuri da zai nemi tilasta wani addini a kan wani ba.” Ya ce ya yi mulki a baya kuma yan nada Kiristoci a muhimman mukamai, sannan su suka fi yawa a cikin gwamnoninsa. Kuma ya ce mafi yawan ma’aikatansa Kiristoci ne, “Idan ban tilasta su shiga Musulunci ba, yaya za a yi in musuluntar da su Amaechi da Okorocha da Oyegun balle sauran ’yan Najeriya?”
A jawabinsa na maraba Shugaban Majalisar Limaman Katolika na Najeriya, Bishop Ignatius Kaigama, wanda har wa yau shi ne Akibishop na Jos ya ce majalisar limaman cocin Katolika ta yi Imani da hadin kai da ci gaban wannan kasa, kuma tana jin takaicin babban gibin da ake samu a tsakanin shugabanni da jama’a. Ya yi fata tattaunawar za ta kasance manuniya ta yunkurin samar da wata kafa ta ci gaba da sadarwa a tsakanin bangarorin.
Bishop-Bishop din sun nuna damuwa kan faduwar darajar ilimi a Najeriya da yaduwar cin hanci da rashawa da hare-hare da kuma tabarbarewar tsaro a kasar nan da sauran matsaloli.
 Da yake mayar da martini Janar Buhari ya ce rashin aikin yi ne umul haba’isin wadannan matsaloli. Ya ce, “A kasar da mafu yawan matasanta ba su da aikin yi, kuma babu alamun sauki a kusa, dole ne a samu irin wadannan matsaloli. Ku samar musu da dama; ku nuna musu gobensu tana da kyau, dukkan wadannan za su zamo tarihi.”
Janar Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tsara tare da bullo da ingantaccen shirin noma tare da bunkasa yankunan karkara domin a jefi tsuntsu biyu da dutse daya wajen inganta noma da karfafa arzikin jama’a da kuma rage kwarara daga karkara zuwa birane.  Ya ce hako ma’adinai zai taimaka wajen samar da aikin yi.
Game da cin hanci da rashawa Janar Buhari ya nanata cewa, “Muna da dokoki da hukumomin da aka dora musu alhakin yaki da cin hanci da rashawa. Abin da muke bukata mu farfado da wadannan hukumomi tare da sanya su yi aiki yadda ya kamata.”
Ya ce burin Najeriya na ci gaba zai sake dawowa ya bunkasa ba tare ba bata lokaci ba da zarar ya zama Shugaban kasa.