Ba ni da sha’awar komawa Manchetser City -Pep Guadiola

Kocin kulob din Bayern Munich da ke Jamus Pep Guardiola ya ce ba shi da niyyar canza sheka zuwa kulob din Manchester City na Ingila a karshen kakar wasa ta bana. Kafofin watsa labarai sun yi ta rade-radin kocin zai koma City ne ganin yadda kocin City Manuel Pellegrini yake cikin tsaka mai wuya.Tsohon kocin […]

Ba ni da sha’awar komawa Manchetser City -Pep Guadiola
Ba ni da sha’awar komawa Manchetser City -Pep Guadiola

Kocin kulob din Bayern Munich da ke Jamus Pep Guardiola ya ce ba shi da niyyar canza sheka zuwa kulob din Manchester City na Ingila a karshen kakar wasa ta bana.

Kafofin watsa labarai sun yi ta rade-radin kocin zai koma City ne ganin yadda kocin City Manuel Pellegrini yake cikin tsaka mai wuya.
Tsohon kocin FC Barcelona na Sifen Guardiola, kwantaraginsa za ta kare ne a watan Yunin 2016 da kulob din Bayern, amma ganin yadda ake tunanin City za ta raba gari da koci Pelligrini ta sanya wasu ke rade-radin kulob din zai maye gurbinsa ne da Pep Guardiola a karshen kakar wasa ta bana.
“Ina sa ran na cigaba da horar da kulob din Bayren Munich a shekara mai zuwa, don haka masu tunanin zan canza sheka zuwa City ba su ji da kyau ba”, inji Guardiola.
Guardiola dai ya kafa tarihi a kulob din FC Barcelona na Sifen inda ya lashe masu manyan kofuna kafin ya bar kulob din kimanin shekaru biyu da suka gabata.