Ba ni da shirin sauka daga gadon sarauta — Sarkin Norway
Sarauniya Margrethe ta Denmark ta bai wa babban danta, Frederik dama ya dora daga inda ta tsaya.
Sarki Harald na Kasar Norway a wannan Talatar ya bayyana cewa har yanzu ba shi da shirin yin murabus duk da shekarunsa da suka ja.
Sarki Harald mai shekaru 86 ya jaddada aniyyar ce a yayin jawabinsa na farko a bainar jama’a tun bayan sauka da Sarauniya Margrethe ta Kasar Denmark ta yi daga gadon sarauta a makonni da suka gabata.
Ina nan a kan bakar da aka sanni a kai. Na yi wa Majalisar Norway ta Storting rantsuwar saboda haka wannan lamari na tsawon rayuwa, a cewar Sarki Harald kamar yadda kafofin watsa labaran Norway suka ruwaito.
Sarki Harald wanda shi ne basarake mafi dadewa a kan karagar mulki a duk nahiyyar Turai, ya yi wannan jawabi ne a wani taron manema labarai da ya halartar a birnin Oslo tare da dansa, Yarima mai jiran gado, Haakon.
Sarki wanda a yanzu ya shafe shekaru 33 a gadon sarauta, zai cika shekaru 87 a duniya a ranar 27 ag watan Fabarairun 2024.
Harald, wanda a yanzu yake iya tsayuwa da tafiya da taimakon da sanduna, a ’yan shekarun nan an yi masa tiyata a zuciya, sannan ya yi fama da jinya iri-iri wadanda suka shafi matsaloli na numfashi da wasu cututtuka.
Ana ci gaba da alakanta rashin lafiyarsa da kuma tsufa a matsayin dalilai na rade-radin da ke yaduwa kan cewa zai iya bin sahun ’yar uwarsa ta nesa, Sarauniya Margrethe ta Denmark wadda ta yi murabus tana da shekaru 83 a doron kasa.
Bayanai sun ce Sarauniya Margrethe ita ma a baya ta sha nanata cewa ba za ta yi murabus daga Masarautar Danes ba, sai dai a jawabinta na jajiberin sabuwar shekaran nan ta bai wa duniya mamaki, inda ta ce za ta bai wa babban danta, Frederik dama ya dora daga inda ta tsaya.