Ba Nijeriya ce kaɗai ke fuskantar matsaloli ba — Gwamnan Oyo

Mu da kanmu ne za mu yi wa kanmu aikin samun mafita.

Ba Nijeriya ce kaɗai ke fuskantar matsaloli ba — Gwamnan Oyo

Gwamna Makinde na Jihar Oyo

Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya bayyana cewa matsalolin da Nijeriya ke fuskanta ba kanta farau ba kuma ba ita kaɗai ce tilo ba domin akwai ƙasashe da dama a faɗin duniya da ke cikin halin ni ’yasu.

A cewar Gwamnan, “addu’o’in roƙon Allah da kishin kasarmu ta gado wadda ta zamo mana uwa maba-da-mama da kuma soyayyar juna ne za su taimaka wajen tsamo Nijeriya daga matsalolin da suka dabaibaye ta.”

Ya ce “Nijeriya ba ita kaɗai ta samu kanta cikin irin waɗannan matsaloli ba.

“Akwai wasu ƙasashen Duniya daban-daban da suka faɗa tsundum cikin irin waɗannan matsalolin da suka fi wanda Nijeriya ke ciki.

Gwamnan ya fadi haka ne a ranar Alhamis a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Farfesa Olanike Adeyemo ce ta wakilci Gwamnan wajen jagorantar manyan jami’an gwamnati da suka yi tattakin kilomita 2 da rabi a shirye-shiryen bukukuwan murnar cika shekara 64 da Nijeriya za ta yi da samun ’yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba.

Gwamnan ya ce wannan tattakin tafiya a kasa shi ma yana daga cikin addu’o’in roƙon Allah samun mafita ga wannan ƙasa.

Ya ce “mu da kanmu ne za mu yi wa kanmu aikin samun mafita domin babu wanda zai iya yi mana wannan muhimmin aiki.

“Saboda haka ya zama wajibi mu jajirce wajen sadaukar da kawunanmu da roƙon Allah Ya kawar mana da matsalar da ke neman hana ruwa gudu a ƙasar Nijeriya.”

Shugabar Ma’aikatan Jihar, Uwargida Olubunmi Oni da Kwamishinoni da jiga jigan ’yan siyasa na PDP da ke mulki a jihar suna daga cikin waɗanda suka rufa wa Sakatariyar Gwamnati baya wajen yin wannan tattakin daga harabar Gidan Gwamnati zuwa Ofishin Gwamna.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7