Ba rabo da gwani ba: Ta’aziyyar Farfesa Hambali Jinju
A maraicen Talatar makon jiya ce na fara cin karo da labarin mutuwar Farfesan Hausa, Malam Muhammadu Hambali Jinju. Nan take fa na fara neman karin bayani daga abokai da na tabbata suna bibiyar al’amuransa, amma ban samu cikakken bayani ba, kasancewar su ma a lokacin nan suka samu bullar labarin, ta bakina. Don haka […]
A maraicen Talatar makon jiya ce na fara cin karo da labarin mutuwar Farfesan Hausa, Malam Muhammadu Hambali Jinju. Nan take fa na fara neman karin bayani daga abokai da na tabbata suna bibiyar al’amuransa, amma ban samu cikakken bayani ba, kasancewar su ma a lokacin nan suka samu bullar labarin, ta bakina. Don haka sai da safiyar Laraba na ida samun tabbaci, ta kafafen watsa labarai, musamman Sashen Hausa na Muryar Amurka da BBC da Rediyo Faransa. Tabbacin wannan rasuwar ya sanya na ce ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah Ya jikan Malam!’
A wannan rana ta Laraba, bayan na natsa a ofis, sai na fara bincikar tarin hotunana, inda na tsamo daya daga cikin hotunan da na dauki marigayin, a yayin da muka halarci wani taron bunkasa harsunan gida a birnin Damagaran na Jamhuriyar Nijar. Na saka wannan hoto a turakata ta Facebok, kuma na rubuta gajeruwar ta’aziyya kamar haka:
“Allahu Akbar! Ba rabo da gwani ba, kafin a san gwani daga ne! Wannan hoton marigayi Farfesa Hambali Jinju ne, wanda Allah Ya yi wa rasuwa jiya Talata da maraice. Na dauke shi hoton nan ne a Birnin Zender a 2010, yayin gudanar da taron bunkasa harsunan gida. Allah Ya jikansa da rahama, amin.”
Tun daga nan kuwa masoya suka ci gaba da antaya addu’o’i da kalaman ta’aziyya, ya Allah ta turakata ko kuma a nasu turakun na Facebook. Babu shakka Duniyar Hausa ta yi babban rashin gwarzon malami.
Malam Muhammadu Hambali Jinju; kafin rasuwarsa a makon jiya, ya kasance shahararren malamin Harussa, musamman Hausa, wanda ya koyar a jami’o’i daban-daban a Najeriya. Jami’o’in sun hada da Jami’ar Legas, da ABU Zariya da Bayero Kano da kuma Usman danfodiyo a Sakkwato.
Ya kasance marubuci, manazarci kuma zakakuri a fagensa na koyarwa. Shi ne malamin jami’a na farko da ya tsaya kai da fata sai an rika koyar da harshen Hausa da Hausa, maimakon a can baya da aka rika koyarwa da Ingilishi. Ya kasance masani mai jin yarukan duniya sama da guda takwas, wadanda suka hada da Larabci da Rashanci da Faranci da sauransu.
Malamin, wanda aka haifa a ranar 8 ga Mayu, 1934 a garin Jinju da ke cikin kasar Nijar, ya yi wa harshen Hausa gagarumin aiki, musamman ma yadda ya rubuta ingantattun littattafai a harshen. Kadan daga cikin littattafan da ya rubuta sun hada da ‘Rayayyen Nahawun Hausa’ wallafar kamfanin Northern Nigerian Publishing Co., Zariya a 1980 da ‘Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba: Kalmomin Kimiyya da Ilimin Fasaha na Hausa’ wanda kamfanin Fisbas Media Serbices, Kaduna ya wallafa a 1992. Haka kuma ya rubuta wani littafin game da tarihin Musulunci a nahiyar Afrika, mai suna ‘Musulunci a Afirka: Nazari ta Hanyoyin Tarihi da Falsafa Game da Matsalolin Yau’ wanda kamfanin ABU Press ya wallafa a 2001.
Malamin dai ya rasu ne a sakamakon sankarar makoshi da hawan jini, bayan jinyar da ya yi a wani asibitin birnin Yamai. Ranar Talata da misalin karfe biyar na marece ya koma ga Sarki Allah. Ya mutu ya bar matar aure daya da kuma ’ya’ya guda tara. An yi masa jana’iza a garinsu, Jinju.
daya daga cikin dinbin daliban marigayin, Farfesa Ibrahim Malumfashi, da yake nuna alhininsa da rasuwar Jinju, ya shaida wa jaridar Blueprint cewa: “Marigayin ya kasance malamina a jami’ar ABU Zariya a 1984. Bayan na kammala karatuna a can kuma na kama aiki a Jami’ar Usman danfodiyo, a lokacin ana kiranta da sunan Jami’ar Sakkwato, ya kasance shugabana kuma mai yi mani jagora a tsangayarmu.”
Farfesa Malumfashi ya ci gaba da cewa: “Mun yi aiki tare da shi na kusan shekaru 20 har zuwa lokacin da ya yi ritaya daga jami’ar, ya koma garinsa na haihuwa, Jinju. Ya kasance kwararren malami, manazarcin harsuna, musamman ma mai bin diddigin tarihi da asalin al’ummar Hausawa.”
“A matsayinsa na dalibin sanannen malamin tarihin nan, Sheikh Anta Diop, marigayi Hambali ne manazarci na farko da ya fara karyata tatsuniyar nan ta Bayajidda, wanda aka rika alakanta shi da cewa shi ne asalin kafa kasar Hausa. A 1985 ne ya taba rubuta cewa, babu yadda za a yi wannan tarihi ya zama na gaskiya. Ya jaddada cewa koda za a ce Bawo ne ‘makirkirin’ tsarin sarauta a Arewacin Najeriya, babu yadda za a ce shi ne ya kafa kasar Hausa. Ya yi gamsasshen rubutu mai gauni a wannan bangare.” Inji Farfesa Ibrahim Malumfashi.
Baya ga Malumfashi, wasu daga cikin sanannun mutanen da suka tofa albarkacin bakunansu game da ta’aziyyar Jinju sun hada da Farfesa Abdalla Uba Adamu da Farfesa Yusuf Adamu, dukkansu da ke Jami’ar Bayero Kano.
Cikin wadanda suka yi addu’a a kan sakon da na aika a turakata ta Facebook kuwa, sun hada da Mahmud Hambali Muhammad da Ahmad Jibril da Abdul M. Hambali da Hambali Abubakar da Ummu Abdillah Zariya da Sunusi Sani Dala da Muhammad Kabir Adam da Abdullahi Alkwatonawi da Sani Hassan da M.A. Faruk Sokoto da Lawan danjuma Adamu da sauransu da dama.
Allah Ya jikan Farfesa Muhammadu Hambali Jinju da gafara, Ya sanya ya dace. Mu kuma da muka rage, Allah Ya sanya mu cika da ingantaccen imani, idan tamu ta zo, amin!