Ba rashin aiki ke sa mu kidaya buhun gero ba – Matasan Yawuri

Muna son sanin ko adadin geron ya fi ’yan Najeriya yawa ne Masarautar Yawuri da ke a Jihar Kebbi tana ci gaba da karbar baki na gida da waje, sakamakon yadda wadansu matasa suke tashi haikan kan sai sun kirge buhun gero. Masarautar Yawuri wadda daya ce daga cikin masarautu hudu da ke Jihar Kebbi […]

Ba rashin aiki ke sa mu kidaya buhun gero ba – Matasan Yawuri

Matasan Yawuri suna qirga gero don sanin adadin da ke cikin buhu

Muna son sanin ko adadin geron ya fi ’yan Najeriya yawa ne

Masarautar Yawuri da ke a Jihar Kebbi tana ci gaba da karbar baki na gida da waje, sakamakon yadda wadansu matasa suke tashi haikan kan sai sun kirge buhun gero. Masarautar Yawuri wadda daya ce daga cikin masarautu hudu da ke Jihar Kebbi ta zama wurin yawon bude-ido ne bayan da ayarin matasan suka yi gardamar cewa buhun gero ya fi ’yan Najeriya yawa wadansu kuma suka cewa ’yan Najeriya sun fi buhun geron yawa.  Bisa ga wannan ne suka shiga kirga geron  domin sanin iya addadin kwayoyin geron da ke cikin wani buhu mai nauyin kilo 100 a wani majalisi da matasa ke zama kowane yammaci  bayan sun dawo daga ayyukansu na gwamnati ko kasuwanci a garin na Yawuri.

Bayan sun shiga kirga geron jama’a da dama daga nan Najeriya da na kasashen duniya sun rika cewa matasan na  Yawuri, kamar ba su da aikin yi ne ya sa suka shiga wannan muhawawar ta kirga buhun gero.  Saboda haka bayan sun fara kirga buhun, sai maganganu suka fara zagayawa a fadin kasar nan da kuma kasashen duniya, wanda hakan ne ya dada fito da sunan masarautar Yawuri a duniya, inda mutanen jihohin kasar nan da na kasashen waje irin su Jamhuriyyar Nijar da Benin da China da Amurka da sauransu suka nuna sha’awa a kai.

Shugaban majalinsin matasan kuma shugaban kwamitin kirga buhun geron, Ahmad Sarkin Yakin Yawuri, ya ce “A kowace rana tun ranar da muka fara kirga buhun geron nan ina amsa kiran waya daga mutanen da zai kai ashirin daga Jamhuriyyar Nijar da Jamhuriyyar Benin da China da Ingila da Amurka da sauransu.”

Ya kara da cewa jama’ar da ke bugo wayar suna son su san kwara nawa ne ke cikin buhun gero mai nauyin kilo dari.

Saboda irin yadda maganar kirga buhun geron ta janyo ya sa mutane daga kasashen duniya na tattaki zuwa garin na Yawuri domin gane wa idanunsu a cikin makonnin da suka gabata.

Wannan kirgar buhun geron dai ana gudanar da ita ce a Unguwar Katungu da ke cikin garin Yawuri. Haka kuma ya ce, “Duk wanda ya bugo waya yana son ji kwara nawa ne a cikin buhun gero sai in gaya masa cewa ba mu kammala kirgar buhun ba, saboda haka ku jira idan muka kammala za mu sanar da mutanen duniya domin sanin ko kwara nawa ne a cikin buhun gero mai nauyin kilo dari.” Bugu da kari ya ce “A lokacin da muka soma wannan kirga geron mun sha magana cewa ba mu da aikin yi ne, amma jama’a ba su san cewa da yawan matasan da ke zama a wannan majalisa ta Unguwar Katungu na da aikin yi ba, domin akwai likitoci da lauyoyi da malaman makaranta da ma’aikatan ofis na Gwamnatin Jihar da Gwamnatin Tarayya da ’yan kasuwa da kuma sauransu. Ana zama a majalisa daga karfe hudu na yamma bayan sun fara dawowa daga wuraren ayyukansu.” Har ila yau ya ce “Dukan matasan da ke zama a majalisar sun yi karatu mai zurfi kama tun daga difloma zuwa digiri na uku. Domin haka ka ga ba ZA a ce zaman kashe wando muke yi ko rashin aikin yi muke yi a majalisar da muke zama a Unguwar Katungu a garin na Yawuri ba.”

Daga karshe ya ce “Mun samu kimanin wata uku muna kirga buhun geron nan kuma insha Allahu nan ba da jimawa ba za mu kammala kirgar geron, a lokacin ne dukan mutanenNajeriya da na duniya za su ji ko kwara nawa ne ke cikin buhu mai nauyin kilo dari. Saboda haka muna ba jama’a hakuri cewa su dan dakace mu nan da dan wani lokaci.”

A cewar wadansu daga cikin matasan da ke kirga geron sun ce, wadansu na kushe abin da suka sa kansu, amma daga bisani da suka ji ana kiransu daga kasashen duniya sai suka fahimci wannan abin alfaharinsu ne.

Matasan sun ce har yanzu a duniya ba a taba samun wadanda suka zauna suna kirga gero kamar dai yadda suka sa kansu ba don haka wannan babban abin alfahari ne a wurinsu, “muna murna da irin kwarin gwiwar da muke samu a sassan duniya,” inji su.

“Domin gudanar da kirgar yadda ta kamata mun raba kanmu a kwamiti, inda muke da masu kirga hudu da masu karba biyu da masu lura hudu, su dai masu lura, aikinsu shi ne su sanya ido wajen an ware geron da aka kirga ba a hada shi da wanda ba a kirga ba. Akwai wadanda suke karba sun kasu, akwai masu karbar wanda aka kirga daga 1 zuwa 500 da masu karbar daga 1 zuwa 1,000. Suna dai fara zaman kirgar ce daga karfe 4 zuwa 6 ko kuma zuwa 7 na yamma. Akalla mutum 30 ne ke kirgar geron,” inji shi.

Mambar a kungiyar kirgar, Lukman Abubakar ya ce, da shi da sauran masu kirgar suna da muradin sanin adadin gero nawa ne a cikin buhu kilo 100, wannan zai sanya jama’a sanin ainihin adadin.