Ba rashin doka ba ne matsalar Najeriya —Naja’atu
Fitacciyar ’yar siyasa, Hajiya Naja’atu Bala Muhammad, ta ce babbar matsalar Najeriya ita ne rashin wadanda za su tabbatar da bin dokokin kasar sau da kafa. Hajiya Naja’atu ta bayyana hakan ne ta fitaccen shirin Inda Ranka na Rediyan Freedom ranar Alhamis, inda ta ce babu dokar da Najeriya ba ta samar ba, amma abin […]
Fitacciyar ’yar siyasa, Hajiya Naja’atu Bala Muhammad, ta ce babbar matsalar Najeriya ita ne rashin wadanda za su tabbatar da bin dokokin kasar sau da kafa.
Hajiya Naja’atu ta bayyana hakan ne ta fitaccen shirin Inda Ranka na Rediyan Freedom ranar Alhamis, inda ta ce babu dokar da Najeriya ba ta samar ba, amma abin takaici an rasa wadanda za su tabbatar da dokokin sau da kafa.
“Najeriya ba ta da matsalar doka, sai dai rashin samun shugaba nagari da zai tabbatar an bi dokokin sau da kafa.
“Muna da hukumomin ICPC, EFFC, da sauran dokoki masu kyau, domin babu dokar da ba mu da ita [a Najeriya].
“Amma kafatanin kasar an rasa wanda zai tabbatar da kowa na bin dokokin, kuma hakan babbar masifa ce da muke fama da ita.
“Amma ina da yakinin da jajircewa za a iya samun kalilan din da a hankali za su zama masu yawa har wdannan matsaloli su zama tarihi,” in ji ta.