Ba ruwan Buhari da kalaman Mamman Daura —Fadar Shugaban kasa
Batun dakatar da tsarin karba-karba a zaben 2023 da Mamman Daura ya yi ra’ayinsa ne ba na Shugaba Buhari ba.
Fadar Shugaban Kasa ta ce babu ruwan Shugaba Buhari a matsayin da dan uwansa Mamman Daura ya bayyana game da mulkin karba-karba a zaben 2023.
Fadar Shugaban Kasa ta ce ra’ayin na Malam Mamman Daura na cewa a zabi shugabanni bisa cancanta ba a jingine karba-karba, ba ta da wata da alaka da Buhari.
Mahawara kan batun na karba-karba ta barke a fagen siyasar Najeriya tun bayan da Mamman Daura ya ce ya kamata Najeriya ta koma zabar cancanta tunda karba-karba ba ta biya bukata ba.
A wata hira ta musamman da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi, ya ce yana ganin a koma zaben shugabanni bisa cancanta da kwarewa ba tare da la’akari da yankin da dan takarar shugaban kasa ya fito ba.
Tuni dai jam’iyyar APC mai mulki da ma babbar adawa da PDP suka yi watsi da ra’ayin nasa tare cewa ba shi da ikon ya zabar musu yadda za su gudanar da harkokinsu na zaben ‘yan takarar shugaban kasa.
Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu a wata sanarwa ya ce Mamman Daura ba ya bukatar amincewar wani kafin ya bayyana ra’ayinsa ko fahimtarsa a kan al’amura.
Ya ce Mamman Daura dattijo ne dan shekara 80, gogaggen dan jarida kuma tsohon Manajan Darektan daya daga cikin jaridu mafiya fice a Najeriya (New Nigerian), don haka yana da ’yancin mallakar ra’ayinsa da kuma bayyanawa kamar yadda dokar kasa ta ba da ’yanci.
Garba Shehu ya kara da cewa, “A tuna cewa tun farkon hirar [Mamman Daura] ya fada cewa ra’ayin kashin kansa yake bayyanawa, kuma ta kowace fuska ba ra’ayin Shugaban Kasa ko na gwamnatinsa ba ne”.
Sanarwar ta yi zargin rashin adalci da kuma jirkita manufar rihar na BBC a kokarin neman yayata ta ga jama’ar kasar.
“Abubuwan da aka tattauna a hirar sun mayar da hankali ne a kan yadda kasar za ta samar da hanya mafi dacewa na tattaunawar da za ta kai ga yi wa kai hisabi da kuma samar da mafita na demokradiyya mafi fa’ida ga dukkannin ’yan kasa ba tare la’akari da bangaren da suka fito ba.
“Wadannan batutuwan na da matukar muhimmanci ga cigaban demokradiyyarmu, kuma a matsayinsa na kwararren dan jarida, masani kuma dattijo, Mamman Daura ya isa ya bayyana ra’ayinsa kamar yadda wasu suke yi.
Tun bayan watsa hirar da a ciki Mamman Daura ya nemi a yi watsi da batun yankin siyasa ko kabila wajen zaben shugabannin kasa a Najeriya ake ta muhawara.