Ba sanya batsa ke sa littafi karvuwa ba – Anty Ummy

Hajiya Halima Yusuf wacce aka fi sani da Anty Ummy, marubuciya ce da ta wallafa litattafai irin su Da Me Zan Ji da Sirrin Zuciya da Ba Kishiya Ba Ce da Burina da Ni Ko Ita da sauransu. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana cewa rubuta batsa da marubuta ke yi a litattafansu ba shi […]

Ba sanya batsa ke sa littafi karvuwa ba – Anty Ummy

Hajiya Halima Yusuf wacce aka fi sani da Anty Ummy, marubuciya ce da ta wallafa litattafai irin su Da Me Zan Ji da Sirrin Zuciya da Ba Kishiya Ba Ce da Burina da Ni Ko Ita da sauransu. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana cewa rubuta batsa da marubuta ke yi a litattafansu ba shi ne yake janyo hankalin masu karatu su karanta littafi ba. Haka kuma a cewarta, fitar da litattafai da marubuta ke yi kasuwa barkatai babu wata qai’da, shi ya janyo kasuwar litattafan ta cunkushe, da sauran batutuwa da suka shafi harkar rubutu.

 

Aminiya: Za mu so sanin taqaitaccen tarihin rayuwarki?

Anty Ummy: An haife ni a unguwar Yakasai cikin birin Kano a shekarar 1978. Na yi karatun firamare da na sakandire a nan Yakasai. Bayan na kammala ban ci gaba da karatu ba, sai aka yi min aure. Daga baya ina gidan mijina sai na koma karatu inda na yi Diploma a harshen Hausa. A yanzu haka ina tare da maigidana da ’ya’ya bakwai, maza huxu mata uku.

Aminiya: Ya aka yi kika fara rubutu kuma yaushe kika fara?

Anty Ummy: Ni dama tun ina qarama ina son karance-karancen litatatfai duk littafin da na gani zan yi qoqari na karanta. To daga nan na sami kaina ina sha’awar rubutu, duk da cewa ba zan iya cewa ga takamemen littafin da ya ja hankalina na fara karatu ba. A shekarar 1997 na fara rubuta wani littafina me suna Da ME ZAN JI, amma ban buga shi ba, har zuwa wani lokaci da na rubuta xaya littafin nawa me suna NI KO ITA. Wanda na sami labarin daga wata yarinya da muka haxu a mota inda ta ba ni labarinta. Kasancewar ni mutum ce mai son yin tambaya, haka na sa ta gaba da tambaya har sai da na ji labarin gaba xaya har take cewa tana neman marubuta don su buga labarin nata. Nan na amsa mata cewa na fara rubutu duk da cewa ban fara bugawa ba. To tun daga nan kuma sai qofa ta buxe.

Aminiya: Litattafai nawa ki ka rubuta?

Anty Ummy: Na rubuta litattafai da dama sai dai wanda  na sami damar bugawa sun kai 17 waxanda suka haxa da DA ME ZAN JI da Ni KO ITA da BURINA da SIRRIN ZUCIYA da MUGUWAR QAWA da LOKACI NE da ALIYA da saurasu, sai kuma wanda na buga a baya-bayan nan wato KA CE KANA SO NA. A yanzu haka ina kan rubuta wani sabon littafina mai suna ALHINI. Amma dai a yanzu saboda wasu harkoki da na sanya a gaba rubutun ba ya sauri.

Aminiya: Ana zargin ku marubuta akan cewa kun ta’allaqa rubutunku akan jigon soyayya, ga kuma zargin sanya batsa a cikin rubutunku, mene ne gaskiyar lamarin?

Anty Ummy: Ba zan ce ba na rubutu akan jigon soyayya ba, sai dai yawancin litattafaina ina rubuta su ne kan abin da na gani ko kuma na ji labari. Idan na duba na ga abu ne da zai amfani al’umma to sai na faxaxa shi na yi rubutu akan shi. Gaskiya ni jigon soyayya ba a gabana yake ba, ban san sauran marubuta ba.

A gaskiya yin amfani da kalmomin batsa abu ne da bai dace ba, domin na tabbata wanda ya rubuta ko ba yanzu ba sai ya ji kunyar abin da ya rubuta. Akwai kalmomin da za a iya amfani da su waxanda za su bayyana wani abu da marubuci ke son faxi, kuma saqon ya isa kamar yadda ake buqata ba tare da an yi amfani da kalmomin batsa ba. Misali idan marubuci yana so ya nuna mata da miji sun keve. To idan ya bayyana cewa sun shiga xaki, to duk mai hankali ya san abin da ake nufi, ba sai ka yi bayani ba. Kin ga anan kin bar mai karatu ya qiyasta sauran labarin da kansa. Ya kamata marubuta su san cewa ita  fa batsar nan ba ita za ta sa a sayi littafin ba, domin mun rubuta littattafan da babu batsa a ciki kuma sun sami karvuwa, sunanmu ya je inda ba mu je ba. A yanzu haka litattafaina nakan ajiye su a fili idan yarana suna buqata suna xauka su karanta, to da na san akwai irin wannan abin kin ga ba zan bar su su karanta ba. Gaskiya da ma mu tun farko saboda irin hakan ya sa muka san irin riqon da za mu yi wa alqalaminmu.

Aminiya: Waxanne matsaloli marubuta ke fuskanta. Domin wasu na ganin matsalar marubuta tana da alaqa da rashin haxin kai, me za ki ce akan hakan?

Anty Ummy: A baya dai muna da matsalar rashin haxin kai. Sai dai a yanzu muna tunanin irin waxannan abubuwa za su kau domin a yanzu akwai wata qungiya ta marubuta mata mai qarfin gaske wato MACE MUTUM. Wannan qungiya na matuqar qoqari wajen haxa kan marubuta da kuma ci gaban rubutu da sauransu.

Sai kuma matsalar cunkushewar kasuwar littatafan, wanda kuma ba wani abu ne ke jawo hakan ba illa rashin tsayayyiyar qa’ida wajen fitar da litattafai kasuwa. Za ki samu cewa yau an fitar da litattafai sababbi kamar 20, ba za a yi kwana biyu ba sai a sake fitar da wasu 20, to sai ki ga wancan da aka fara fitarwa cinikin ya tsaya an koma kan sabon da ya fito yau. To su ma ba za a yi wani cinikin kirki ba wani zai sake fitowa kasuwa. Dama ita haka kasuwar littafi ta gada, idan littafi ya fito yau aka fara cinikinsa, idan wani ya fito ya fi na jiya haskawa to fa wancan littafin ba zai kai labari ta fuskar kasuwanci ba. Kamata ya yi a samar da wani tsari kamar yadda ’yan fim xin Hausa ke yi ya zama cewar a wata guda za a fitar da littatafai kamar 10 ba za a sake fitar da wani ba sai wata na gaba. Kin ga wata gudan nan ya ishi waxancan litatatfan su ci zamaninsu. Haka kuma bayar da hayar littattafai da ake yi da kuma karanta littafi da ake yi a gidajen rediyo duk sun kawo cunkushewar kasuwar littatatfai.

Aminiya: Wane kira ki ke da shi ga ’yan uwanki marubuta?

Anty Ummy: Ina shawartar ’yan uwana marubuta da su riqa rubuta alheri, ya zama cewar mun rubuta litattafan da za a yi amfani da su a bayanmu. Yanzu ga wasu litattafan nan ana sanya su a manhajar karatu. Irin wanann ne zai sa mutun ya ci gajiyar rubutu, amma ba wai a karanta littafin a ji daxi a yi dariya a qarshe a yar da shi ba. Ya kamata marubuta mu bar son zuciya da tunanin kyautatawa masu karatu. Kada ya zama cewa marubuci ya bar masu karatu su jagorance shi. Idan ya zama masu karatu ke jagorantar marubuci to za a yi varna. Idan ka fitar da littafi na xaya sai masu karatu su riqa kiranka cewa ga yada ya kamata na biyun ya kasance, to ba haka ake yi ba, domin watakila idan marubucin ya biye ta son ran masu karatu, to sai ki ga an yi ba daidia ba. Ya kamata ya zama cewar marubuci ne ke jan linzamin jigon labarinsa. Akwai buqatar idan aka sami sabon marubuci ya miqa littafinsa ga wani wanda ya daxe a harkar domin duba masa shi.

Aminiya: A yanzu ana yawan mayar da litattafai zuwa finafinai, ko kina ganin hakan a matsayin ci gaba?

Anty Ummy : Wanann abu ci gaba ne, domin dama su ’yan fim ai da bazar marubuta suke rawa. Sai dai a wasu lokutan idan an zo batun sasantawa tsakanin marubuta da masu fim sai ki ga an sami son zuciya a harkar. To kamata ya yi a sami kyakkyawar alaqa tsakanin juna don a gudu tare a tsira tare.

Aminiya: Wane marubuci ne gwaninki?

Anty Ummy: Dukkanin marubuta suna burge ni, kuma ina jinjina musu, sai dai ba ni da kamar Bala Anas Babinlata, saboda irin baiwar hikimar iya rubutu da Allah ya ba shi. A lokuta da dama idan ina rubutu nakan yi qoqari na kwaikwayi salon rubutunshi. A vangaren mata kuma ina son rubutun Rahma Abdulmajid. Sauran marubuta ma suna qoqari don babu littafin marubucin da ba na karantawa.