Ba saukar gaggawa jirgin IRS ya yi a Kaduna ba – Fola Akinkotun

A karshen makon jiya ne aka ruwaito cewa wani jirgin saman kamfanin IRS ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Kaduna, sai dai Shugaban Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta kasa Injiniya Fola Akinkotun ya ce saukar da jirgin ya yi ba ta gaggawa ba ce.Injiniya Akinkotun ya bayyana wa manema labarai a Legas cewa […]

Ba saukar gaggawa jirgin IRS ya yi a Kaduna ba – Fola Akinkotun
Ba saukar gaggawa jirgin IRS ya yi a Kaduna ba – Fola Akinkotun

A karshen makon jiya ne aka ruwaito cewa wani jirgin saman kamfanin IRS ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Kaduna, sai dai Shugaban Hukumar Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta kasa Injiniya Fola Akinkotun ya ce saukar da jirgin ya yi ba ta gaggawa ba ce.
Injiniya Akinkotun ya bayyana wa manema labarai a Legas cewa wasu daga cikin manema labarai sun baza labarin cewa jirgin ya yi saukar gaggawa alhali ba haka ba ne.
Ya ce a aikinsu na tukin jirgi shi ne da farko jirgin iyakarsa Kaduna, kuma bai wuce ko gaza  lokacin da ake sa ran ya sauka ba, kuma ya ce lokacin da jirgin ya sauka bai lalace ba, kuma bai  ji wa koda fasinja daya rauni ba.
Ya ce abin da ya faru shi ne lokacin da jirgin ya zo sauka direbansa ya gano cewa man da ke gurza taya ta fito tana da matsala, shi kuma ya sanar da dakin ba da iznin saukar jirgi cewa ga matsalar da yake fuskanta amma zai yi kokarinsa, kuma daga baya tayoyin sun fito jirgin ya sauka lafiya.
Injiniya Akinkotun ya yi kira ga jama’a su yi watsi da duk abin da za su ji game da sauka ko tashin jirgi matukar ba daga hukumar ko masana harkar tukin jirgi ba ne, domin haka na iya shuka tsoro a zukatan matafiya ta jirgin sama, wanda hakan kan iya jawo babban koma baya ga tattalin arzikin kasa.
Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na IRS, Alhaji Rabi’u Isiyaka Rabi’u ya ce duk da yake cewa kowa na da ’yancin fadin albarkacin bakinsa, to amma a rika fadin magana mai ma’ana da in wani ya ji zai amfana.  Ya ce Kamfani IRS ya kwashe shekara 12 yana aiki a kasar nan, kuma bai taba yin hadari ba, sai dai matsala daya ko biyu da ba a rasa ba.
Game da cewa jirgi daya kamfanin ke da shi, sai ya ce, “Wannan ba gaskiya ba ne, muna da jirage da dama, amma muna amfani ne da wanda muke da kwarin gwiwar cewa ba ya da matsala,”