…Ba sayenmu gwamanti ta yi don mu janye yajin aiki ba – kungiyar Direbobin Tanka
Mataimaki na biyu a shiyyar Fatakwal na kungiyar Direbobin Tankar Fetur ta kasa, wato PTD, Alhaji Abdullahi Akomaye , ya ce ko kusa gwamnati ba ta sayi bakinsu ba suka janye yajin aikin da Hadaddiyar kungiyar Ma’aikatun Hakar Manfetur da ta direbobin (NUPENG) suka yi makon jiya, a sakamakon lalacewar hanyoyin sufuri na kasar nan, […]
Mataimaki na biyu a shiyyar Fatakwal na kungiyar Direbobin Tankar Fetur ta kasa, wato PTD, Alhaji Abdullahi Akomaye , ya ce ko kusa gwamnati ba ta sayi bakinsu ba suka janye yajin aikin da Hadaddiyar kungiyar Ma’aikatun Hakar Manfetur da ta direbobin (NUPENG) suka yi makon jiya, a sakamakon lalacewar hanyoyin sufuri na kasar nan, wanda ya sanya su ala tilas suka yi yajin aikin, domin jawo hankalin gwamnatin tarayya, ta yadda za tasan halin da direbobin tanka da kuma ma’aikatansu ke ciki, musamman idan sun yi dakon danyen manfetur, domin kaiwa kasuwanni, motocin na yawan yin hadari su kama da wuta, lamarin da aka kiyasta ana asarar sama da Naira 111.
Mataimakin ya karyata haka a hira da Aminiya, inda ya ce “Babu wani bakin mu da gwamnati ta saya ko ta ba mu toshiyar baki mu janye yajin aiki da muka yi. Wannan zargi ba gaskiya ba ne, amma mutane masu zargi ba za su zo su yi tambaya ba, kamar kai yadda ka zo kana yi ba haka abin yake ba, babu wani kudi ko toshiyar baki da aka bamu.”
Da ya juya kan dalilan da suka sanya su janye yajin aikin, Alhaji Akomaye ya ce mun cimma matsaya tsakanin mu da gwamnati, inda aka debi wa’adin wata biyu za su gyara hanyoyi da suka lalace da ma mun shiga yajin aikin ne saboda hanyoyi ne, ba wai don mu musguna wa wani ko wasu ba ne. Idan har ba a cika musu alkawari ba, akwai bukatar kungiyar su ta sake zama domin tunatar da gwamnati alwashin da tasha, in ba haka ba, kuma abin da kungiyar su ta yanke shawara shi za su bi.