Ba shi ne abin da matasa ke bukata ba – Lauya Mainasara

Aminiya ta tuntubi Lauya Mainasara Ibrahim Faskari domin jin  ta bakinsa game da wannan yunkurin da ake yi na ba matasa tallafin kudi. Ga abin da ya ce: Aminiya: An gabatar da kudirin a rika bai wa matasa tallafin Naira dubu biyar amma kuma majalisar dattijai ta yi watsi da kudurin, ya kake kallon wannan […]

Ba shi ne abin da matasa ke bukata ba – Lauya Mainasara
Ba shi ne abin da matasa ke bukata ba – Lauya Mainasara

Aminiya ta tuntubi Lauya Mainasara Ibrahim Faskari domin jin  ta bakinsa game da wannan yunkurin da ake yi na ba matasa tallafin kudi. Ga abin da ya ce:

Aminiya: An gabatar da kudirin a rika bai wa matasa tallafin Naira dubu biyar amma kuma majalisar dattijai ta yi watsi da kudurin, ya kake kallon wannan mataki da suka dauka?
Barista Mainasara – Kudirin ba wai yana da madogara cewa tilas a matsa wa shugaban kasa ya ba duk wanda ba ya da aikin yi Naira dubu biyar ba ne, domin wannan ba ya cikin tsarin mulki, a tsarin mulki akwai sashi na biyu da ake ki kira directibe principle of state policies, ma’ana kudurori ko manufofi wadanda kasa za ta ginu a kai, to a nan ne aka yi magana cewa gwamnatin kasa za ta ginu a kansu, yadda za ta yi ta tabbatar da aikin yi ga matasa ta tabbatar kuma ga wadanda ba su da aikin yi an samu hanyoyin tallafa musu yadda ba za su tagayyara ba a kasar nan. Wannan shi ne daya daga cikin alkawurran da wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ko kuma jam’iyyar APC ta yi yaki har aka zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari.
To bayan da ya hau kuma a yanzu, kai ba za ka yi wa gwamnatin adalci ba ka yi tunanin a wannan matakin a ce za a fara aiwatar da wannan shirin a yadda kasa take a gurfan? an riga an yi kaca-kaca da kasar nan, har ta kai ga albashi ma ba a iya biya, bayan haka kuma farashin man fetur wanda kasar nan ta dogara da shi kacokan a kasuwannin duniya ya fadi kasa warwas. Bayan nan kuma saboda halin da kasar ke ciki, shi kanshi shugaban kasa da mataimakinsa suka ce a rage albashinsu su rika karbar rabi, su ’yan majalisa ana batun a rage nasu abubuwa da suke samu, amma da yawa sun ce ba za su yarda a cire musu ko kwabo ba. Bayan nan kuma gwamnatocin jihohi na samun matsala wajen tafiyar da ayukansu saboda babu kudi, har sun gurfana a gaban shugaban kasa suna neman a ba su tallafi wanda za su biya basusukka da kuma yadda za su yi tsare-tsaren abubuwan da za su fara yi.
Bayan nan kuma idan aka yi la’akari da yadda ita kanta gwamnatin tarayya take ciki, ba ka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari adalci ba a ce wajibi ne a biya, saboda ko da sun zantar da wannan kudurin akwai kudirin da ko da kun zantar da shi zai zama na shirme, domin idan sun zantar da kudurin ba su samu hadin kan biyu bisa uku ba na ’yan majalisar dattawa da na ’yan majalisar wakilai ba, to ba kuduri ne wanda yake da wajabcin cewa dole sai an aiwatar da shi ba. Akwai kudiri wanda yake na shawara ne, akwai na wajibi wanda yake idan an zantar da shi dole a aiwatar da shi, don yana daidai da karfin doka, amma wannan kudiri ne da ake son a yi tuni, kuma ba wai tuni ne na sai an zantar da shi a zauren majalisa ba,. Akwai abubuwa daban-daban da ‘yan kasar nan yanzu suke bukatar ‘yan majalisa su yi dokoki masu mahimmanci, maimakon mayar da hankali kan abubuwa wadanda suke ba za su yiwu ba.
Nayi murna da aka yi fatari da wannan kudurin, domin ba yanzu ne ya kamata a kawo wannan ba, a bari bawan Allah nan da makarrabansa su gano bakin zaren da  za a bi domin tattalin arziki Najeriya ya gyaru, hadin kan kasar nan ya samu, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar nan ya wanzu, sanan kasashen duniya su shigo da jarinsu, mu samu arzikinmu ya bunkasa. Mu rarraba hannunmu daga dogara kan man fetur, mu bunkasa aikin gona da zakulo ma’adanan da suke kasa, to a wannan lokacin ne idan arziki ya tabbata daga nan sai mu dawo mu ce a sake fasalin tsarin kasar nan, mene ne  ya kamata ya zama albashin da mutane za su rika dauka, me ya kamata har wadanda suke hidimar kasa (NYSC) su dauka, da dai sauransu.
A yi tunanin wadansu hanyoyi da za a bullo wa marasa karfi, don a baya an sha kawo irin wannan tallafi amma sai ka ga ana samun matsala, mafi dacewa da matasa shi ne a ba su aikin yi, ba wai a rika ba su kudi ba.