Ba Tambuwal ne dan takararmu na Gwamnan Sakkwato ba – PDP

Jam’iyar PDP a Jihar Sakkwato ta ce har yanzu ba ta canja shawara kan wanda zai yi takarar Gwamnan Sakkwato ba, abin da ake ganin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai yi takarar sabanin Alhaji Maniru Muhammad Dan Iya da jam’iyar ta zaba tun farko. Shugaban jam’iyar a Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Milgoma ne ya tabbatar […]

Ba Tambuwal ne dan takararmu na Gwamnan Sakkwato ba – PDP

Jam’iyar PDP a Jihar Sakkwato ta ce har yanzu ba ta canja shawara kan wanda zai yi takarar Gwamnan Sakkwato ba, abin da ake ganin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai yi takarar sabanin Alhaji Maniru Muhammad Dan Iya da jam’iyar ta zaba tun farko.

Shugaban jam’iyar a Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Milgoma ne ya tabbatar da haka a zantawarsa da manema labarai a Sakkwato, ya ce mutane su fita batun jita-jitar da ake yadawa wai PDP ta canja dan takara.

Milgoma ya ce in har mun canja dan takararmu za mu sanar bayan mun cika ka’idojin da hukumar zabe ta shardanta, har yanzu akwai lokaci, ya kamata a jira amma har yanzu ba wani sauyin dan takara.

Shugaban PDP din ya ce sun kira taron ne kawai don su gode wa wakilai kan hadin kan da suka ba su a zaben fitar da gwani na Shugaban Kasa da na jiha ba don tabbatar da Tambuwal ba “Muna da dan takararmu kowa ya sani Manir Dan Iya ne, kawai mun kira su ne mu yi musu godiya Sakkwato ta Matawalle ce kowa ya sani in har zai yi takara shi ke da nasara da yardar Allah,” inji Milgoma

To amma sai dai wani jigo a Jam’iyyar PDP ya shaida wa Aminiya cewa hakika a ranar Lahadin da ta gabata da dare jam’iyyar a jihar ta kira wakilanta na dukan kananan hukumomi 23 inda suka hadu a sakatariyarta aka tantance su da zimmar za su yi zabe don tabbatar da takarar Gwamna Tambuwal, amma lokaci ya kure ba za a iya gudanar da zaben 12 na dare ba ta wuce ba, kan wa’adin da hukumar zaben ta bayar na mika saunayen ’yan takara kan wanan sai aka dakatar da shirin. Idan an bude kofar musayar ’yan takara sai a sanya sunan Tambuwal maimakon Maniru da ya janye takararsa da kashin kansa ba wata tursasawa.

Ganin yadda Jam’iyyar PDP a jihar ta ga shirinta na farko na neman wargajewa a haka aka kara tabbatar da Tambuwal zai dawo ga shirinsa na biyu ne na in bai samu tikitin takarar Shugaban Kasa ba ya dawo takarar Gwamna, abin da ya sanya aza Dan Iya ya rike masa takarar, abin da dukan ’yan jam’iyyar suka aminta da shi.

Dawowar Gwamna Tambuwal takarar Gwamna ya faranta wa al’ummar Sakkwato musamman magoya bayan Faruk Malami Yabo da suke son a kada dan takarar Wamakko kan zargin rashin adalci da dauki dora da suke ganin ya yi a jam’iyarsu ta APC.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa