Ba wanda zai karbi mulki daga Buhari ya tabuka wani abu a kwana 100 —Shehu Gabam

Gwamnatin Buhari ta yi ta kokari don samar makiyaya iri-iri amma aka yi ta adawa.

Ba wanda zai karbi mulki daga Buhari ya tabuka wani abu a kwana 100 —Shehu Gabam

Alhaji Shehu Musa Gabam, Makaman Tilde shi ne Shugaban Jam’iyyar SDP ta Kasa, a tattaunawa da Aminiya kan cika kwana 100 na Gwamnati Bola Ahmed Tinubu ya tabo batutuwa da dama da suka shafi kasar nan da siyasarta kamar haka:

Sama da kwana 100 da wannan sabuwar gwamnati ta fara mulki, kuma bisa ga al’ada ana auna gwamnati a kwana 100 na farkon mulkita, a matsayinku na ’yan adawa yaya kuke kallon abin da gwamnatin ta yi a wadannan kwanaki?

Ala kulli halin in mutum zai yi bayani ya gaya wa kansa gaskiya. Gaskiyar kuwa ita ce duk wanda ya karbi gwamnati ko da ba APC ta gaji kanta ba, ko PDP ko SDP ko wata jam’iyya ta karbi mulki daga hannun Buhari, za ta samu matsalar gudanar da gwamnati.

Saboda an karbi gwamnatin da matacciya ce, an karbi gwamnatin da babu tsaro, an karbi gwamnatin da yunwa ta addabi al’umma, gwamnatin da noma ya yi kasa saboda rashin tsaro.

An karbi gwamnatin da akwai ’yan gudun hijira ko ta ina, gwamnatin da marayu suka yi yawa a kasar, gwamnatin da ba a taba zalunci da dukiyar Najeriya kamar na zamaninta ba, gwamnatin da kan ’yan Najeriya bai taba rarrabuwa kamar na zamaninta ba, na Arewa kadai yadda suke kashe kansu suke garkuwa da kansu ba mu taba shiga irin wannan hali ba.

To duk wanda ya karbi gwamnati a wannan hali, in za ka yi wa kanka adalci ka kalli yadda kasar ke ciki da yaje-yajen aiki na malaman makarantu da na asibitoci da ’yan kwadago a kasa za ka ga tattalin arzikin kasar gaba daya a kasa yake.

Kuma an zo an shiga rikicin zabe don haka babu wanda zai iya yi maka wani abu fitacce a cikin kwana 100.

Tunda Bola (Tinubu) ya karbi mulki yake ta kokarin yaya za a yi a zauna lafiya.

Ya karbi mulki an cire tallafin mai a cikin kasafi, cire tallafin nan ya jawo tsadar abinci da matsaloli da yawa.

Wanda ya karbi kasa akwai ci gaba ne za ka tambaye shi a cikin kwana 100 me ya yi?

Amma irin Bola me zai iya yi maka a cikin kwana 100 a yanayin da ya karbi Najeriya?

Ya fara ne cikin wahala, ya fara da canja manyan hafsoshi don ya ga an kawo tsaro, tsaron nan har yanzu a lalace yake.

A Abujar nan kusan kullum garkuwa da mutane ake yi. ’Yan tasi ma yanzu kusan kullum satar mutane suke, Babban Birnin Kasar nan ke nan fa.

Ka dubi Kaduna su Bauchin nan kullum garkuwa da mutane ake yi.

Wannan ita ce maganar gaskiya, ba maganar siyasa ba ce, an karbi kasa gurbatacciya, abubuwa sun lalace, don haka ni ban yi tunanin akwai abin da zai iya yi cikin kwana 100 ba, sai dai in yaudari kaina, kamar yadda wasu suka yaudari kansu suna zaton su ga ya yi wani abu.

Yanzu yana so ne ya ga gwamnati ta zauna. Duk masu zuba jari sun bar kasar nan, ana kokari a ga yaya za a yi a dawo da zaman lafiya na siyasa, yaya za a dawo da hadin kan ’yan Najeriya kowa ya yarda kasa daya ce.

Don haka ko wa ya karba yana da matukar wahala ya yi wani abu da za ka yaba ka ce ya yi wani fitacce guda daya.

Kana ganin matakan da ya dauka kan abubuwan da ka fada ya kamo hanyar fitar da Najeriya daga halin da take ciki?

Na farko maganar tallafi, mun yarda dama babu tallafi a Najeriya, cuta kawai [ake].

Shi kansa tsohon Shugaba Buhari lokacin da yake kamfe ya ce babu wani tallafi cuta ce, ya ce ya yi Ministan Mai a baya. Amma a kan wannan cuta ya gama mulki.

Sannan mun ce in akwai tallafin su NNPC da suke biya, su fito su ce ga kamfanoni da suka biya wannan tallafi.

Kuma bincike ya nuna almundahana ce, tsohuwar Minista Ngozi Iweala sun yi bincike sun nuna almundahana ce.

Amma saboda wadanda suke wannan abu sun fi karfin kasar suna da dukiya da komai, za su iya kawo fitina a kasar kowa na tsoron su.

To in kana tsoron su, don me za ka nemi mulkin Najeriya?

Najeriya da take da al’umma fiye da miliyan 200, mutane kalilan da ba su kai kashi daya ba, sun sa ka cikin fitina.

Sannan kowace kasa ta duniya tana bayar da tallfi. Wasu kasashe suna bayar da tallafi a kan ilimi wasu a kan noma, wasu a harkar lafiya, wasu a harkar fetur.

To da (Tinubu) ya zo cire tallafin, yadda ya cire ne ba mu yarda da kwaf daya a cire gaba daya ba.

Domin shi ya jawo fitinar tsadar rayuwa, buhun masara ya koma Naira dubu 60 da wani abu, ba a taba wannan a Najeriya ba.

Yunwa ta sake shiga kasar saboda yadda aka cire tallafin.  Komai da za ka saya [ya yi tsada] saboda kudin mota ya tashi.

Ma’aikatan gwamnati da ake biyan su misalin Naira dubu 40 ko dubu 30, in ka cire kudin mota, albashin ya kare ba ka maganar kudin abin da za ka ci da iyalinka.

An cire tallafin kamar kabewa aka yi, maimakon a bi a hankali ana tafiya ana gyara, ana bincikar wadanda suke cutar Najeriya ta hanyar wannan tallafi.

Na biyu, mun yi masa maganar ya binciki CBN duk wanda ke da hannu a cutar Najeriya a hukunta shi, to yana wannan bincike.

Har yanzu ba a gano kan matsalar tsaro ba, amma wannan ba laifin Gwamnatin Tarayya ce kadai ba, da laifin gwamnoni a ciki.

Ba yadda za a yi kana Gwamna kana babban jami’in tsaro a jiha, dokar kasa ta ce kwamishinan ’yan sanda ya yi aiki a karkashinka ya karbi umarni daga wajenka, amma a kauyuka abubuwa suna faruwa ba ka sani ba.

Mutumin da ke kauye ba ya da lambar da zai kira gwamna ko kwamishina ko ciyaman ya yi korafi, abu na faruwa a kauye da yake, ta ina za a samu zaman lafiya?

Sai kowane gwamna ya yarda zai yi aikinsa na gwamna zai saurari al’umma ne kadai zai iya zaman lafiya, in ba haka ba shi ma kansa ba zai zauna lafiya ba.

Maganar jami’an tsaro suna bin sa aiki banza ne. In al’umma suka yi bore ba abin da jami’an tsaro kalilan da suke bin ka za su iya yi masa.

Kuma babu abin da ke kawo bore a kasa illa yunwa da fatara da tashin hankali.

Da ka yi wadannan maganganu, bayan dawowar mulkin farar hula a 1999, PDP ta yi mulki, APC tana yi, ba ka ganin rashin akida a fannin tattalin arziki ke jawo wannan?

Ba shi ba ne. Da ni aka kafa PDP tun tana G7 lokacin marigayi Abubakar Rimi a gidansa a Kaduna.

Daga G7 aka je G8, zuwa G18 da G34 aka mayar da ita jam’iyyar siyasa ta kasa.

Abin da ya faru an samu kura-kurai a lokacin, sannan gwamnatin soji ta Janar Abdulsalami Abubakar tana da sha’awa.

Maimakon a bar kwararrun ’yan siyasa wadanda a tarihinsu sun yi hulda da al’umma sun yi zaman lafiya da jama’a, cikin al’umma suka tashi, sai aka ce a’a, don a dadada wa wasu kan abin da ya faru a lokacin zaben 12 ga Yuni, a mayar da mulki Yamma a samu wani Bayarbe a sa.

Matsalar ba wai Bayarbe ba ne, akwai ’yan siyasa fitattu a cikin Yarbawa, amma sai aka ce a dauko Obasanjo da ke kurkuku a kawo shi.

To dan siyasa na asali da ke shiga kauyuka ya san matsalolin jama’a an jingine shi, daga nan PDP ta rikice.

Sannan aka yi ta lallabawa aka zo Solomon Lar ya zama shugaban jam’iyyar na farko. Fitaccen dan siyasa ne, amma Obasanjo ya yi waje da shi.

A cikin karamin lokaci aka cire shugabannin jam’iyyar wajen biyar ana canza su.

Sannan a gwamnoni ba a dauko fitattun ’yan siyasa ba, sai aka kawo wadanda suka yi kwangiloli da soja suka samu kudi, wadanda ba su san darajar siyasar ba.

Ta ina za ka san ana da tsari na samun nasara yadda kake tunani? Wannan na cikin abubuwan da suka jefa mu a halin da ake ciki a siyasar Najeriya.

Na biyu, gwamnonin yawanci sun zo da niyyar tara kudi ne ba yi wa al’umma aiki ba.

Shi ya sa in ka duba cikin gwamnonin da suka yi aiki guda hudu ko biyar ne za ka ce sun yi fice a aiki.

Misali a Arewa maso Gabas, kana son Ahmadu Mu’azu ko ba ka son sa ya yi aiki a Jihar Bauchi.

In ka san tarihin Bauchi kafin ya zama gwamna ba ka isa ka ce Mu’azu bai yi aiki ba. Da an same su da yawa da ba a shiga halin da ake ciki ba.

Kuma in ka cire mulkin soja, ka gaya min daga kan Obasanjo ayyukan da suka yi.

Yanzu Abujar nan ka dube ta gaba daya su Dandalin Eagles da Sakatariyar Tarayya kusan kashi 70 lokacin soja aka yi.

Saboda haka ’yan siyasa su suka zalunci kasar, saboda ba su koyi darasi kan yawan juyin mulkin da soji suka yi a kasar ba.

Shi ya kawo mu gabar da muke ciki a yau, ’yan siyasa sun kasa, ana zalunci, ana kashe mutane, a shiga gida a sace mutum, ’ya’yan mutum su hada baki da ’yan uwa su sace mahaifinsu ko dan uwansu.

A da in aka ce za mu tashi a Arewa mu rika sace ’yan uwanmu ba zan yarda ba.

In aka ce ’yan Najeriya za su shiga halin da za su sace ’yan uwansu su yanka su ba zan yarda ba, yau shi muke ciki tsundum.

Har yanzu ba a samu shugabanni wadanda kasar ce a gabansu ba.

In ka dauki lokacin Shagari an daidaita al’amuran mulki saboda sun kawo kwararru sun sa su a kujerun mulki, an samu ci gaba.

Amma yau wane ne ya daidaita al’amura ya yi kokarin yin abin da Shagari ya yi? Shekara nawa ke nan?

To yana da sauki mutum ya zauna ya ce wane ke da laifi.

Jam’iyyar PDP da ta kamata ta kawo shugabanci na adalci, an bar lalatattun mutane sun karbe shugabancinta, shi ya sa ta fadi, shi ya kawo wannan lalacewa, an saki ginshikin wadanda suka kafa PDP, azzalumai sun zo sun kwace ta sai dauki-dora suke yi ba abin doka, shi ya kada PDP, to haka APC take yi.

Don haka in ba an samu shugabanni masu adalci da al’umma ke gabansu ba da wahala a fita daga wannan fitina.

Kuma dole talakan da ake zalunta ya yarda zai yi abin kirki ga kansa.

Don me mutum zai zo ya ba ka Naira 5,000 ko 10,000 ka san ba za ka sake ganin sa ba sai wani zabe?

Da hankalinka da tunaninka, ka ki zaben wanda zai taimaki rayuwarka.

In kana kishin kasa da al’ummarka, dole ka zabi wanda ka tabbatar cewa yana da tarihin kirki kuma zai taimaka.

Amma in ka zabi dan kwangilar da ya tara kudi, ya zo ya ba ka ka karba kuma ba a kawo maka ci gaba ba, ba a yi maka asibiti ba, ba ruwan sha, ba kwalbati, ba hanya, kai ka cuci kanka.

Arewa za ta fita daga cikin wannan kunci ne in mutane suka zabi wanda shi ne alheri a gare su ba wanda zai zo da kudi ya ba su kowa ya zo yana kuka; wannan ya sa Arewa ta fi ko’ina talauci a Najeriya.

Ka ce akwai kura-kuran gwamnoni a batun tsaro. Akwai masu cewa matsalar tsaro na da alaka da talauci, kuma talaucin ya yi kamari ne saboda danne kudaden kananan hukumomi da gwamnonin suke yi. Kana ganin hakan ya taimaka wajen haifar da matsalar tsaro?

Ai ba wai ya taimaka kadai ba ne, shi ne ginshikin talaucin. Gwamnoni ne suka kashe kananan hukumomi.

In ka tuna kafin Buhari ya sauka an yi kokari a ba kananan hukumomin ’yancin kudadensu amma ba a samu adadin da ake so ba, wasu gwamnonin sun yi amfani da majalisun dokokin jihohi aka ki amincewa, da dokar da yau babu wannan matsala.

Da suka yaki hakan wa suka yaka? Sun yaki kada al’umma ta samu abin yi ne, sun fi son su yi ta musu bakin mulki.

Amma da an amince da dokar duk kudin da ya shiga karamar hukuma, in ciyaman bai yi aiki ba za a tuhume shi.

Ka je ka bincika kai dan jarida ne, za ka ga yadda ake tura kason karamar hukuma, za ka ga wata karamar hukumar a cikin minti biyu an tura mata kudi an cire su.

Babu gwamnati ce a kasa? Babu jami’an tsaro ne? Babu masu bincike ne a Najeriya? Me ya sa aka bari?

Mene ne aikin EFCC da ICPC? Su je su duba asusun kananan hukumomi, in an tura kudin yaya ake cire su?

Duk yaudarar kanmu muke yi, shi ya sa ba ma son fadar gaskiya.

Babu yadda za a yi alal misali yau ina gwamna in karbi kudin karamar hukuma. Me zan yi da su?

Abin alfahari ne a ga ciyaman ya yi aiki in je in bude aikin. Mulki sauki ne, tsarin da aka yi na shugabanci ba a yi don mutane su wahala ba. An yi don rayuwar al’umma ta zauna cikin sauki ne.

In ka dauko yadda za a gudanar da mulkin ka ajiye a gaban teburinka ka ce sai kai kadai ba za ka gama lafiya ba.

Kudin karamar hukuma kowace na da kasafin ayyukan da za ta yi. Amfaninka na Gwamna ka tabbatar an yi wadannan ayyuka ka rika sa ido.

Ba wannan kudi ne zai sa ka yi arziki ba, wannan kujera da Allah Ya ba ka in kai mai godiyar Allah ne ta ishe ka.

Amma ka rika taba hakkin al’umma da ke karamar hukuma, wadanda a kanta suka dogara ba za ka gama lafiya ba.

Kansiloli ba su san aikinsu ba, domin yadda ake da majalisar jiha akwai ta karamar hukuma da ke sa ido.

Wannan ne abin da gwamnoni ba sa so, sun kashe sun lalata shi.

Najeriya ta shiga wani mummunan hali mutane na baro karkara, ba kananan hukumomi suke zuwa ba, jihohin ma suna bari su yi Abuja don neman abin da za su ci.

Don haka matukar al’umma ba su yarda a gyara ba, matukar majalisun jihohi ba su yarda a yi gyara ba, suka tsaya suna tilasta abin da zai faru su da gwamnoni, suka manta daga kauyukan nan aka zabo su zuwa majalisun, ba sa tunanin talauci da bala’in da mutane suke ciki a kauyuka, Allah Zai tambaye su!

Kuma dadin me suke ji al’ummarsu na cikin fitina? An hada baki da su an ki a taimaka wa al’umma.

In kananan hukumomi suka samu ’yanci Najeriya za ta ci gaba, kananan hukumomin za su rika samar da kudin shiga, su rika ba jihohi.

Sannan in aka gyara kundin Tsarin Mulki jiha za ta samu kudin shiga saboda arzikin da Allah Ya ajiye a kasa.

Cikin wannan kudi, jiha za ta biya bukatunta kuma ta ba Gwamnatin Tarayya, amma gaba za a zauna lafiya?

Ana jingina ayyukan assha da dama ga Fulani, a matsayinka na Bafulatani yaya kake ji a ranka?

Ba gaskiya ba ce a ce Fulani ne kawai, ai rikicin manoma da makiyaya bai taba muni haka, ba sai zamanin Buhari.

Akwai kungiyoyin ’yan banga da suka haddasa rikicin, ka je ka karanta tarihin rigimar Katsina da Zamfara, shin Fulani ne suka fada musu suna kashe su, ko Fulani ne suka sace shanu da awakinsu?

Bafulatani bai ce a kai masa ruwan famfo gidansa da ke daji ba, bai ce a kai masa wutar lantarki ko a yi masa hanya zuwa gidansa da ke daji ba.

In ya sayar da saniyarsa za a cire haraji a ciki, in ya sayar da kaza ko nononsa za a cire haraji, amma gwamnati ba ta dauki mataki lokacin da ake kwace dukiyarsu ana kashe su ba.

Duk mutumin da ya ga ba hukumar da take kare shi, zai kare kansa.

Lalacewar mulki ya jawo wannan, ta yaya in an samu barna a gona ’yan banga za su dauki makami su kashe mutum?

Sannan me ya sa ’yan sanda in sun kama Bafulatani ba za su bayar da belinsa ba, sai ya sayar da shanunsa ya ba su kudi kafin su sake shi? Shi ba ya da ’yanci ne, shi ba dan Najeriya ba ne?

Saboda haka zalunci ne ya jawo wannan fitina.

A da ba a samun rigimar manoma da makiyaya ne? Bafulatani in ya yi maka barna ka kai kara zai iya sayar da saniyarsa ya biya, me ya canza?

An sace shanun Bafultani gaba daya sana’ar da ya sani an bar shi yana yawo a titi, ’yan iska sun jawo shi cikinsu, sun bar shi da shaye-shaye, sannan sun san yana da zuciyar fada, sun dauki bindiga sun ba shi.

Bafulatani zai iya shafe shekara guda ba ya da Naira dubu biyu, an tura shi ya je ya tsare hanya ya samu Naira miliyan daya, miliyan biyu, me zai koma ya yi maka a daji?

Gwamnati ba ta sani ba ne ko babu rahoto a kan haka? Sannan malaman da suke shiga ruga-ruga suna wa’azi, me ya faru, me ya hana?

Ai ba gwamnati daya tsarin mulkin ne aka juya shi sama da kasa. Kuma wannan na da mummunan hadari wanda ya shafe mu kowa bai iya magana.

Akwai masu cewa gwamnonin wannan jamhuriyya sun fi karfin Shugaban Kasa ta yadda in suka hade baki sai yadda suka ga dama ake yi, kuma hakan ne ya sa da suka nemi a mika musu kananan hukumomin aka mika musu.

Kana ganin haka ne?

Sai dai lalatacen Shugaban Kasa ne zai bari gwamnoni su fi karfinsa.

In ka samu lalataccen Shugaban Kasa matsoraci ne zai bari gwamnoni su fi karfinsa.

Tsarin Mulkin Najeriya ya sa babu shugaban wata kasa da ke da karfi irin Shugaban Najeriya. Ai mun ga mulkin Obasanjo, lokacin da gwamnonin suka fara rashin mutunci da rashin hankali, ya yi maganinsu, shi ba mutum ba ne?

Kowane gwamna sai da ya koma cikin taitayinsa. Akwai dokokin da za ka bi ka cire Gwamna a tsarin mulki. In ya zalunci al’ummar jiharsa Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da karfinta ta sa a cire shi don ya zama darasi ga saura.

Buhari ya bar wannan ya sa gwamnoni suka dauka ba wani sai su. Ya yanke shawara gwamnoni su ki, babu abin da ya yi, yana Shugaban Zartarwa na Najeriya.

Ba yadda za a yi gwamnoni su fi karfin Shugaban Kasa, in yana tare da Majalisar Dokoki ta Kasa, ba wanda ya isa ya yi masa wani abu.

Sannan kudin da ake ba gwamna na jiha ne ba nasa ba, dokar jiha ta ce majalisar jiha ta bincike ka, me ’yan majalisar jiha ke yi?

In kana da kwararrun ’yan majalisa masu kishi za su bar Gwamna ya rika cutar su?

Matsalar ita ce, mun hadu mun lalace ana cutar da mu, an sa wa jama’a talauci, mutum bai isa ya yi magana ba, saboda an ba shi Naira dubu daya ko yana tsoron za a zo a kashe shi, yunwa na damun sa, an hana shi yin noma, buhun taki yau Naira dubu 30, ta ina zai iya noma?

In noma ya gagara, ta ina kadai ce za ta kawo zaman lafiya ba, malamai da sarakuna me suke yi don kawo zaman lafiya a Arewa?

Duk Bafulatanin da ya dade a waje, ba wanda bai san shi ba a wajen.

Sannan in bakon Bafulatani ya zo daga wani waje, al’ummar wajen sun san bako ne. Me ya kawo ba a hada kai a yi gyara?

Wuraren da ake fada a kasashen Yarbawa da Ibo da sauransu Fulani ne?

Lokacin Jonathan akwai abubuwan da aka so a yi, amma aka kawo son zuciya aka kashe maganar.

Bafulatani in aka kwashe masa shanu ya dace a rage masa asara, ka ce eh wannan an zalunce shi yaya za a yi mu farfado da shi?

Kamar yadda Shugaba ’Yar’aduwa ya yi wa mutanen Neja-Delta, gwamnati za ta iya sayo shanu ta ce duk wanda ya rasa nasa, ga shanu biyar ya je ya fara kiwo, wannan zai rage fitina.

Amma ba abin da yake yi, ba karatu yake ba, ba sa ’ya’yansa karatu yake ba, ba ilimi ba tarbiyya ba, malaman da suke zuwa su yi masa wa’azi ma yau babu, me ake so ya yi?

Gwamnatin Buhari ta yi ta kokari don samar makiyaya iri-iri amma aka yi ta adawa, me za ka ce?

Shugaban Kasa na da ikon ya yi haka, shi ya sa ake kiran sa da Shugaban Zartarwa. Ba za ka kawo irin wannan gaban majalisa ba, za ka yi ne a matsayin tallafawa.

Bankunan da ake tallafa musu kada su ruguje ba kudin talakawa ba ne?

Fulanin da ake tatsar nonon shanunsu ba su bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin Najeriya ne?

In ka tallafa musu a matsayin tallafi ga bangaren kiwo laifin me ka yi?

Dama Shugaba Buhari ba ya da niyya ce, kawai da ya kawo abin aka yi masa adawa ya watsar.

Da ya watsar me aka yi, fitinar ba ci gaba ta tyi ba? Bankunan da kuke daukar kudin Najeriya ko kai musu dauki wannan ba laifi ba ne?

Sannan mene ne laifi a yi makiyaya ta zamani (Ranch) ga shanu a rika samar da madara a daina shigo da ita daga waje?

Labukan shanu sun zama gonaki da gidaje, wace hanya za a bi a dawo da su don magance matsalar?

Da gangan aka yi haka. Misali a gidanka in ka yi aure daki daya za ka fara zama, in ka hayayyafa a daki dayan za ka ci gaba da zama kai da ’ya’yanka?

Rashin tsari ne, ya kamata a san yawan jama’a na karuwa kuma in ya karu za a bukaci wuraren kiwo da na noma da gidaje.

Dole in yawan jama’a ya karu a bude sababbin wurare, amma babu wanda ya damu da wannan saboda ba su damu da rayuwar mutane ba.

To in ba ka damu da zaman lafiyar mutane ba, yaya za a yi ka zauna lafiya?

Da da ake zaman lafiyar ai an yarda a zauna lafiya ne. A yau in ka ce ba zan zauna lafiya ba, yaya za a yi ka zauna lafiya?

Me ya jawo wannan?

Duk lalacewar mulki ne.

A baya in aka samu matsala, sarakunan kauye ke sasantawa yau duk babu, me ya jawo haka, me ya lalace haka? Mece ce mafita ga wadannan matsaloli?

Duk wanda ke da shekara 40 zuwa sama a kasar nan ya san tarihin Arewa, ya san yadda rayuwa take gudana, ya san hanyar tarbiyya ta Arewa, ya san yadda muke da al’adu da dabi’u, dole a koma a yi tunanin yaya za a gyara.

Na biyu hanyar da kawai za a iya canja gwamnati a dimokuradiyya ita ce ta hanyar zabe.

Dole ne ’yan Arewa in muna so rayuwarmu ta canja, mu daina yarda ana sayen kuri’unmu lokacin zabe.

Al’umma su fito su zabi wanda ya cancanta, dimokuradiyyar nan ta je har kauyuka kan kansila.

Duk wanda ke da tarihin zalunci da sata kada jama’a su zabe shi.

In aka zabi gurbatattun mutane ta yaya za su san matsalolinku su kai majalisa a warware su?

Na uku dole Gwamnati Tarayya ta ayyana dokar ta-baci a harkar samar da abinci ta samar da taki da sauran kayan noma don a yaki yunwa wadda ta addabi mutane.

Na hudu, mutanen Najeriya da ’yan Arewa su yi hakuri da dadi da babu dadi su noma abin da za su ci, domin kada a samu kai a cikin matsalar ga yunwa ga rashin abinci.

In kana da abin da za ka ci, ya fi a ce ba ka da kudin sayen abinci.

Zuciyarmu ta mutu, yaranmu sun kewaye ko’ina babu abin da suke yi ban da roko.

Yaro da karfinsa da komai ba zai koma ya taimaki kansa ya taimaki iyayensa ya yi noma ko ya tallafa ba.

Na karshe shugabanni su ji tsoron Allah, gwamnoni su ji tsoron Allah, su san cewa babu abin da zai tabbata a duniya.

Yau akwai gwamnonin da muka sani suna neman abin da za su ci ne, ga su nan a fili.

Akwai wadanda suka yi mulkin, yau ba su san halin da suke ciki ba, alherin da ka yi shi zai bi ka. Allah Ya ba ka mulki amma ba ka taimaki jama’a ba.

Maleriya ta kashe mutum a kan maganin Naira 2,000 da ka gaza saya ka kai asibiti a ba mutanen da ba za su iya saya ba, ka ce fitina ba za ta fado mana ba?

Muna ta kashe mutane a ce fitina ba za ta fado mana ba? Tarbiyyar da muke da ita, in dan Arewa ya ga maraya yakan dauka ya kula da shi, yau ina wannan?

Na yi almajiranci na san wannan, ba wanda zai ce ban sani ba. Me ya sa wannan ba ya faruwa a yanzu? Me ya samu imaninmu?

Babu mutum daya da zai yi wannan gyara dole sai mun taru kowa ya ba da gudunmawa.

Najeriya za ta iya gyaruwa cikin kankanen lokaci, amma sai mun zabi shugabanni nagari, sabanin haka ban san wata mafita ba.