Ba wani shiri na tsige ni-Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya yi watsi da rahotannin da suka nuna majalisar dokokin jihar na shirin tsige shi. Gwamnan ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokokin jihar saboda haka babu rashin fahimta tsakaninsa da ’yan majalisar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema […]

Ba wani shiri na tsige ni-Badaru

Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya yi watsi da rahotannin da suka nuna majalisar dokokin jihar na shirin tsige shi.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokokin jihar saboda haka babu rashin fahimta tsakaninsa da ’yan majalisar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawar sirri da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.