Ba wani yunkuri na tsige Gwamnan Jihar Bauchi – APC
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ya karyata rade-radin da ke yawo a jihar cewa wai ’yan majalisar jihar 31 suna yunkurin tsige Gwamnan Jihar Barista Mohammed Abubakar daga kan kujerarsa, saboda yadda gwamnatinsa take tafiyar hawainiya tun lokacin da ya kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun bana.Alhaji Uba […]
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ya karyata rade-radin da ke yawo a jihar cewa wai ’yan majalisar jihar 31 suna yunkurin tsige Gwamnan Jihar Barista Mohammed Abubakar daga kan kujerarsa, saboda yadda gwamnatinsa take tafiyar hawainiya tun lokacin da ya kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun bana.
Alhaji Uba Nana ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi a karshen makon jiya. Ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne, wasu marasa kishin jihar ne suke yayata wannan farfaganda a tsakanin al’umma. “Muna kira da babbar murya ga ’ya’yan Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi su guji yada jita-jita domin duk wanda jam’iyyar ta samu yana yayata karya tabbas za ta ladabtar da shi,” inji shugaban.
Ya ce Jam’iyyar APC reshen jihar ta amince da murabus din da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Musa Adamu Lar, kuma ta gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin.
Daga bisani ya ba da sanarwar dakatar da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Jihar Alhaji Shu’aibu Isma’il Rahama daga kujerarsa. Alhaji Rahama tsohon dan majalisar dokokin jihar ne daga karamar Hukumar Toro.