Ba yakin neman zabe Sanata Atiku ya soma ba – dan Zamawa
Wani na hannun daman Sanata Atiku Bagudu, Alhaji Aminu Umar dan Zamawa ya ce rangadin da Sanatan mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya ke yi a jihar ta sada da zumunta ce ba ta neman zabe ba. dan Zamawa ya ce yin wannan bayani ya zama wajibi ganin jita-jitar da wasu masu neman tsayawa takarar mukaman […]
Wani na hannun daman Sanata Atiku Bagudu, Alhaji Aminu Umar dan Zamawa ya ce rangadin da Sanatan mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya ke yi a jihar ta sada da zumunta ce ba ta neman zabe ba.
dan Zamawa ya ce yin wannan bayani ya zama wajibi ganin jita-jitar da wasu masu neman tsayawa takarar mukaman siyasa suke yadawa saboda sun razana da dubban mutanen da ke tarbar Sanatan a duk inda ya nufa.
Alhaji dan Zamawa ya ce Sanata Atiku Bagudu yana yin abin da ya saba yi ne tun lokacin da aka zabe shi Sanata yau shekara shida, inda a lokacin kowace Sallah yakan ziyarci Sarkin Gwandu Janar Muhammadu Iliyasu Bashar da Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera da Sarkin Yawuri Dokta Muhammadu Zayyanu da kuma Sarkin Zuru, Janar Muhammadu Sani Sami, inda bayan ya ziyarci sarakunan yakan gana da ’yan siyasa tare da tallafa wa jama’a.
Ya ce Sanata Atiku dan siyasa ne da ke kusantar talakawa, tunda aka zabe shi bai taba gudu zuwa Umara ko kasar waje kamar yadda ’yan siyasa ke yi don kaurace wa jama’arsu a daidai irin wannan lokaci da mutane ke bukatar tallafi daga ’yan siyasa.