‘Ba ’Yan al-Shabab ne suka kai harin Kenya ba’
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ba ’yan kungiyar al-Shabab ba ne suka kai mummunan harin da aka kai garin Mpeketoni, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 60. Mista Kenyatta ya dora alhakin harin kan ’yan siyasar yankin, inda ya ce an kai shi ne kan wata kabilar kasar. Yawancin wadanda suka […]
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ba ’yan kungiyar al-Shabab ba ne suka kai mummunan harin da aka kai garin Mpeketoni, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 60.
Mista Kenyatta ya dora alhakin harin kan ’yan siyasar yankin, inda ya ce an kai shi ne kan wata kabilar kasar. Yawancin wadanda suka mutu a harin ’yan kabilar shugaban kasar ne, wato kabilar Kikuyu. A lokacin harin, maharan sun ware wadanda ba Musulmi ba, inda suka kashe su nan take.
Wani mutum ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa mata 12 ne wadanda suka kai harin suka sace, lokacin da suka kai harin a garin Poromoko, wanda ke kusa da garin Mpeketoni.
kungiyar ba da Agaji ta Red Cross ta tabbataar da cewa mutum takwas ba a san inda suke ba sakamakon harin da aka kai ranar Lahadi. Akwai kuma wasu karin mutum 50 da suka bace.
Sai dai kungiyar al-Shabab ta bayyana cewa itace ta kai harin, inda kuma ta ce ta yi hakan ne saboda kasancewar dakarun Kenya a Somaliya da yadda dakarun ke kashe Musulmi.
Kenya ta aika da dakarunta zuwa makwaciyyarta Somaliya a shekarar 2011, saboda ta taimakawa dakarun Majalisar dinkin Duniya domin yakar ’yan kungiyar masu zafin kishin Islama ta al-Shabab.