Ba za a biya lakcarori kudin aikin da ba su yi ba

Ministan Ilimi ya karyata zargin da ASUU na cewa biyan su na iya kwanakin da suka yi aiki yunkuri ne na mayar da su ma’aikatan wucin gadi.

Ba za a biya lakcarori kudin aikin da ba su yi ba

Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada matsayinta cewa ba za ta biya malamam jami’a ladar aikin da ba su yi ba.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana haka ne a tsokacinsa kan zanga-zangar lumanar da malaman jami’a suka yi kan biyan su albashin iya kwanakin da suka yi aiki a watan Oktoba, bayan sun janye yajin aikinsu na wata takwas.

“Babu wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba; amma an janye yajin aiki kuma gwamnati ta riga ta yi abin da ya kamata.” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Matsayin gwamnati shi ne babu wanda za ta biya albashin kwanakin da bai yi aiki ba, saboda haka aka biya su iya kwanakin da suka yi aiki.”

Adama Adamu, wanda ya yi jawabi bayan taron Majalisar Zartaswa ta Kasa a Fadar Shugaban Kasa ya ce, abin da gwamnati ta biya lakcarorin ya yi daidai da dokar ‘ba aiki, ba biya’.

Da aka tambaye shi ko gwamnati za ta tattauna da kungiyar ASUU domin guje wata sabuwar matsala, ministan ya ce, “ba ni da masaniya kan wata matsala.”

Ya kuma yi watsi da zargin da Shugaban ASUU na kasa ya yi na cewa biyan su iya kwanakin da suka yi aiki wani yunkuri ne na gwamnati ta mayar da su ma’aikatan wucin gadi.

A ranar 16 ga watan Oktoba ne lakcarorin suka janye yajin aikinsu na wata takwas bayan Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya shiga tsakani a takaddamar Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU da Gwamnatin Tarayya.

Bayan sun janye yajin aikin, a karshen watan gwamnati ta biya su iya kwanakin da suka yi aiki a watan.

Sai dai ASUU ta ce hakan ya saba ka’ida tun da su ba ma’aikatan wucin gadi ba ne amma gwamnati  ta ce abin da Dokar Kwadago ta tanada ke nan.