‘Ba za a rushe shaguna a Mararrabar Gurku ba’
Mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarawa shawara kan Hukumar Raya Biranai (NUDB) Hassan Ogbole Abari ya musanta rade-raden da ake yi cewa za a rushe shagunan bakin titi a garuruwan Marabar Gurku da Masaka da ke karaman Hukumar Karu da ke jihar.Hassan Abari ya ce ya dade yana ji wannan labari amma hakan ba gaskiya […]
Mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarawa shawara kan Hukumar Raya Biranai (NUDB) Hassan Ogbole Abari ya musanta rade-raden da ake yi cewa za a rushe shagunan bakin titi a garuruwan Marabar Gurku da Masaka da ke karaman Hukumar Karu da ke jihar.
Hassan Abari ya ce ya dade yana ji wannan labari amma hakan ba gaskiya ba ne sai dai akwai wasu ’yan rumfuna da ba a yi su akan tsari ba, su ne za a rusa su, ba manyan shaguna mutane ba. Ya ce sai kuma batun kasuwar Ado wadda aka kawo musu zane da rokon a ba su dama su rusa wasu shaguna domin samun tsari mafi kyau a kasuwar, “Mun yi musu ’yan tambayoyi kan batun ’yan kasuwa masu amfani da shaguna a kasuwar, sun ce sun zauna da ’yan kasuwar kuma sun yarda. Bayan haka muka ce su kawo mana rubutacciyar takarda mai nuna amincewar ’yan kasuwar kuma sun kawo mana, kuma kada a mance kasuwar Ado a karkashin karamar Hukumar Karu take, ba ta jiha ba ce. Saboda haka idan aka ga wani lamarin rusau a kasuwar Ado ba Hukumar NUDB ba ce su da kansu ne za su yi abinsu,” inji shi.
Abari ya shawarci al’umma su kasance masu bin dokar gwamnati na kauce wa yin gini kusa da titi domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya jinjina wa Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura kan irin kokarin da ya yi na tsarawa da tsabtace biranen jihar.