Ba za a tilasta wa kowace jiha ta samar da makiyaya ba – Audu Ogbe

A yayin da wadanda jihohin kudanci da kuma wadansu jihohi a arewacin kasar nan ke korafi game da yunkurin da gwamnati yi na kebe wuraren kiwo ga fulani makiyayan  a jahohi, Ministan ma’aikatar gona, Cif Audu Ogbe ya yi karin haske game da al’amarin. Ministan ya bayyana a Yola cewa yanzu gwamnati ta gano yadda za […]

Ba za a tilasta wa kowace jiha ta samar da makiyaya ba – Audu Ogbe

Cif Audu OgbeA yayin da wadanda jihohin kudanci da kuma wadansu jihohi a arewacin kasar nan ke korafi game da yunkurin da gwamnati yi na kebe wuraren kiwo ga fulani makiyayan  a jahohi, Ministan ma’aikatar gona, Cif Audu Ogbe ya yi karin haske game da al’amarin.
 Ministan ya bayyana a Yola cewa yanzu gwamnati ta gano yadda za ta magance rikici  tsakanin makiyaya da manoma ta hanyar  kebe wajen kiwon shanu, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga Lamidon Adamawa a fadarsa.
 Audu Ogbe ya kara da cewa,  jihohin da ba su yarda a kebe wuraren kiwon dabbobi ba, ba za a tirsasu ba. “Me ya sa mutane suke yin haka, kamar ba su cin nama?” inji shi.
 Ya ce gwamnati na son kebe wani wuri a kowace jiha domin makiyaya su samu inda za suyi  kiwon dabbobinsu ba tare da zuwa wani waje ba.
 Audu Ogbe sai bukaci  a ba su hadin kai wajen kebe wani wuri da za a gyara domin samar da abinci ga dabbobi saboda makiyaya su samu inda za su zauna tare da dabbobinsu, yadda makiyaya Fulani za su daina zuwa wadansu wurare don nemo abinci ko ruwa ga dabbobinsu.“ Gwamnati na iya kokarinta don neman yadda za ta magance wadannan matsalolin kuma ba za ta tirsasa kowace jiha ba idan ba ta son makiyaya.”Inji shi.
 Ya ce bai kamata a rika daukar makami ana kashe mutane ba, don haka ne gwamnati ke son kebe wani wuri a gyara domin samar da ruwa da abincin dabbobi, domin Najeriya na da filaye da dama da za a ware wa makiyaya.
A karshe ya shawarci ‘yan Najeriya da su daina kawo harkar addini da kabilanci  a harkar, domin samun cigaban kasa kuma makiyaya su samu wajen kiwon dabbobinsu.