Ba za a yi amfani da mu a tarwatsa kasar nan ba – ‘Yan Shi’a

A tattaunawar da shugaba Buhari ya yi da manema labarai ya yi tsokaci kan arangamar da aka samu tsakanin sojoji da mabiya mazahabar Shi’a a garin Zariya. Malam Yakubu Yahaya Katsina wanda yake  jagorancin mabiyan na Al Zakzaky a halin yanzu ya shaida wa Aminiya irin yadda suka dauki wannan jawabi na shugaba Buhari, tare […]

Ba za a yi amfani da mu a tarwatsa kasar nan ba – ‘Yan Shi’a
Ba za a yi amfani da mu a tarwatsa kasar nan ba – ‘Yan Shi’a

A tattaunawar da shugaba Buhari ya yi da manema labarai ya yi tsokaci kan arangamar da aka samu tsakanin sojoji da mabiya mazahabar Shi’a a garin Zariya. Malam Yakubu Yahaya Katsina wanda yake  jagorancin mabiyan na Al Zakzaky a halin yanzu ya shaida wa Aminiya irin yadda suka dauki wannan jawabi na shugaba Buhari, tare yin bayani a kan wadansu al’amura da suka shafe su:

Aminiya: Me za ka ce game bayanin da Shugaba Buhari ya yi game da rikicin da ya faru a Zariya?
Malam Yakubu:  To da farko dai ita matsalar data faru a Zariya a ranar 12 ga watan 12 na shekarar 2015 abu ne na bakin ciki da damuwa kwarai da gaske wanda bai kamata ya faru ba, amma kuma ya faru. To sai dai dole tambayoyi da yawa za su taso. Ko ba komai shi shugaban kasa shi ne wanda alhakin tsaro ya rataya a wuyansa, na ran kowane dan Najeriya,kuma mu ba mu bambanta da sauran mutane ba, muma ‘yan Najeriya ne, saboda haka rayuwarmu ma yakamata a ce an kare ta. To amma akwai bam mamaki akan amsar da shugaban ya bayar acikin wannan tattaunawa da aka yi da shi,wanda ya nuna dama kamar yana da masaniya a kan duk shirye-shiryen da aka yi. Saboda haka sai ya yi ta kauce wa fadin wani abu takamaimai. Alal misali,ana iya tambayarsa, yaya za a yi ana kashe mutane a kasarka a dauki awa kusan 24,amma ba ka ce komai ba? Har sai wannan rana da aka yi hirar da shi aka ji bakinsa, bayan an yi wajen kwana goma sha daya da yin wannan abin. Saboda haka amsar da shugaban kasa ya bayar ba ta gamsar da mu ba,kuma ba ita ce yakamata ya bayar ba a matsayinsa na shugaban kasa. Kamata ya yi ya yi bayani, idanma bai sani ba ne ya fito ya ce bai sani ba. Idan kuma ya sani me ya sa aka yi awa 24 ana kashe mutane kuma bai ce komai ba? Ka ga zai zamo da yawunsa ke nan. Saboda haka,amsar da ya bayar ba ta gamsar da mu ba gaskiya.
Aminiya: Shugaban kasa ya ce ba zai yi azarbabi ba saboda ya san akwai kwamitin da gwamnatin jahar ta Kaduna ta kafa don bincike, duk da wannan bayani nasa ku a wajenku bai yi wani abu ba?
Malam Yakubu: Hakika a jaha ne abin ya faru. Amma jaha ke da sojoji? Wa ke da soja,waye kwamandan sojoji,wa ke bada damar a yi harbi? A ka’idar kasa,shugaban kasa ne kawai ke da iko ya bayar da dama a harba harsashi, hasalima shi ne Babban Kwamanda. A nan ba maganar jaha ake yi ba, tunda soja ne suka fito suka yi harbi. Hasali ma,ta hannun wakilinsa shugaban sojoji aka yi harbin. Ka ga yakamata ya yi wani abu tunda ba magana ba ce ta jaha. Ko da ‘yansanda suka yi wani,duk da cewa suke cikin jama’a kowane lokaci,nan ma dai hakki ne na shugaba, duk da ga wakilansa can. Amma da su ‘yansanda ne suka yi,hankalinmu zai iya zuwa ga gwamnatin jaha,saboda gwamnatin jaha tana aiki da ‘yansandan jaha a kan duk wani abin da ya shafi farar hula. Amma wannan soja ne fa suka fito da Kwamandansu na kasa suka yi wannan aika-aika, sannan kuma ya fito ya ce mene ne? Wannan ba uzuri ba ne.
Aminiya: Ana ganin cewa kamar mabiyanku sun raina dokar kasa ne shi ya sa duk abin da suka ga dama suke yi?
Malam Yakubu: Babu maganar raina dokar kasa. Wace doka muka karya? Idan ka ce taro ne na wa’azi ko gamgami, ai tsarin mulki ya lamince da yin haka, saboda kana da ‘yancin ka yi taro ko gamgami, har ma a ba ka kariya. Ba ka  bukatar izni domin ka yi jerin gwano,sai dai ko idan su jami’an tsaro sun ga cewa wannan yana da matsala, to sai su bi shi a baya. Idan ya rikice ya zamo wata matsala ko rigima ko wata hayaniya, to akwai hanyoyin da ake bi. Sai su sanya amsa-kuwa(loud speaker)su yi sanarwa ta gargadi ko kuma su nemi shugabannin wannan gamgami ko taro su tattauna da su, idan ba su bari ba,to sai su dauki abin da a turance ake cewa,’minimum force’,wato mafi kankantar mataki don tarwatsa wannan taro, ciki kuwa har da fesa barkonon tsohuwa(tier gas). Amma wannan an zo da bindigogi ne kawai ana harbin mutane. Ke nan abin ba maganar tare hanya ba ce. Kuma yin muzahara hakkinmu ne, doka ta lamince, kuma mu yana da alaka da addininmu. Don idan mutum ya karanci tarihin addinin musulunci zai ga Manzon Allah(SAW)ya yi muzahara tare da sahabbansa a wata rana a Makka, wadda su kuraishewa suka sa wuta suka zagaye Ka’aba don kada a zo inda take,su kuma nan suka taso,lokacin da aka zo kusa da Ka’aba har Zaidu Bn Harisu yana cewa,a kare Manzon Allah. To tun da Manzon Allah ya yi haka kuma har ya bar duniya bai ce kada a yi ba, muna da hujja a cikin addininmu. Idan ma mutum bai samu littafin da zai karanta ba,ya samo wannan fim na “The Message”,wanda wani mutumin Siriya ne ya shirya, wanda kuma shi ba dan Shi’a ba ne balle a ce yana goyon baya ne ya kawo. Llittafi ya karanta kuma ya mayar da shi fim. Ka ga a ce maganar raina hukuma wannan ba maganar kamawa ba ce. To mene ne raina hukuma. Na farko dai, ka ga tun da tsarin kasar nan yake tafiya, yau sama da shekaru 100 da zuwar Bature inda ya dankara mana tsarinsa wanda ya yi hannun riga da namu na musulunci,wane korafi muka yi? Muna sa ‘ya’yanmu makarantar da bature ya tsara,muna yankar takardun mota,muna bin kiliya hannun dama,ana kafa dokar fita a ranar da ake sharar karshen wata mu ki fita daga gidajenmu har sai wa’adin da aka bada ya cika,kai har kotu muna zuwa mu kai kara,muna aikin gwamnati,to wace doka muka karya? Muna da ‘yancin yin gamgami da muzahara da kowane irin taro, domin dokar kasa ta ba mu dama. Babu daya daga cikin dokokin kasar nan da muka karya. Watakila mutane za su ga kamar muna karya doka ne ko kuma taurin kai, idan aka ce yanzu nan Allah ya ce a yi kaza, amma ya saba wa manufar gwamnati,kamar yanzu abin da shi Buhari ya yi na cewa za a hana sanya hijabi. Hijabi dokar Allah ce, kuma aya ce. To ka ga shi yanzu yana cewa suna tunanin hana hijabi idan maslaha ta nuna hakan a kasa,mu kuma a ayar Alkur’ani an wajabta mana sa hijabi,a matsayinmu na musulmi me yakamata mu yi? Masu tuhumar mu muna da taurin kai su karba wannan tambayar. Allah ya ce a yi Buhari ya ce kada a yi. To a irin wannan ne ake ganin muna da taurin kai,amma idan ba a irin wannan ba,komai tare muke tafiya da kowa.
Aminiya: Maganar hana sa hijabi da shugaba Buhari ya yi,ya kawo ta ne bisa sharadin idan matsalar da ake fuskanta ta cigaba,addini ma kuwa ya yarda da lalura.
Malam Yakubu: To na farko dai abin da muke so mutane su fahimta shi ne, kasar nan dai akwai wadanda suke da sha’awa a kanta. Akwai wadansu kasashen da sun sa wa Najeriyar nan ido kuma suna bukatarta ko ta halin kaka,hasalima har sun ayyana mata shekarar wargajewa har zuwa 2015,wanda kuma daidai lokacin wargajewar ne gare su ta yi. Saboda haka suna neman kowace irin kafa da za su wargaza Najeriya. Sun kafa gwamnatin baya ta PDP kuma ta fara biya masu bukatunsu, sun kamo hanya mataki-mataki har inda za su wargaza Najeriya din, har lokacin da Buhari ya shigo da karfinsa,wannan karfin ya sa suka karbi abin da ke zahiri,suka ga cewa lallai kam zarihin abu ne, suka yarda suka mika masa mulkin,amma fa tsare-tsarensu da suka ba waccan gwamnatin ko suke yi ta karkashinta yana nan bai kau ba, kuma shi ne yanzu suke cigaba da shi. Saboda haka kar ka yi tsamanin wai za su daina. Yanzu ma ya bude masu kofa. Yanzu ne za su cigaba da sa wa mata hijabi su sanya masu bom domin su tayar da shi,su kuma suna kara yawan wannan, shi kuma yana kara daukar matakan hana sa hijabin. Tarko ne suka yi masa wanda zai fada a ciki ko kuma ya riga ya fada a ciki, gaskiyar magana ke nan. Wadannan masu sa wa mata hijabi da bom ba musulmi ba ne,babu yadda za a yi musulmi ya sanya wa jikinsa bom ya nufi masallaci ko coci ya tayar da shi. Addini ba ta’addanci ba ne, a karanta tarihinsa a gani. Saboda haka duk abin da suka yi a baya bai ba su natijar da za su yi nasara ba, saboda haka sai suka ga akwai wadansu mutane da ake kira ‘yan Shi’a da ake gani kamar ko suna da tsauri ko taurin kai ko idan an yi masu ba su hakuri,saboda haka bari su tabo su yadda za su fusata su taimaka a wajen wargaje kasar. Wannan dalilin ne ma ya sa mu tun farko ba mu da wani shiri na tayar da hankali a kowane sashe na tsare-tsarenmu, domin ba za mu taimaka a wargaza kasar nan ba, amma suna so su fake da mu su yi amfani su tunzura gwamnati a kanmu,mu kuma su yi mana abin da zasu yi mana, mu kuma mu harzuka ta yadda ko dai mu dauki makami ko mu yi kone-kone ko kashe-kashe. Shike nan sai su samu dama ta hanyarsa sai a wargaza kasar, su kuma su samu abin da suke so,to mu ba za mu yi wannan ba. Duk wani abin da suke tunani za mu yi,to ba za su samu ba. Ba mu rike makami,ba mu bugun kowa balle mu kashe ko mu kona kayan wani. Dalili shi ne,ba mu so kasar ta wargaje, muna so ta tsaya a dunkule yadda take. Su kuma masu sha’awa a kan kasar ba za su cim ma muradunsu ta hanyarmu ba. Tunzura mu da aka yi ana so ne mu fusata,can ga Biyafara ta taso ga ‘yan Neja-Delta, sai kuma nan a ce ga ‘yan shi’a,sai ta kwabe,idan kuwa kasa ta kwabe shike nan sai fadace-fadace,daga nan sai yaki, su kuma sai su samu abin da suke bukata.
Aminiya:  Kana maganar cewa ku masu son zaman lafiya ne, amma kuma sai ga makwabtan shi Zakzaky a Zariya suna murnar kama shi da aka yi tare da ruguza wajen taruwar taku,domin a cewar mazauna Gyallesun a da kamar suna gidan Yari ne,yaya za mu kwatanta wannan?
Malam Yakubu: Yauwa! Su wadannan mutane masu fadin haka muna ganin wadansu mutane ne da aka yi hayarsu domin su yi hakan. Muna da labarin wata kungiya wadda lokacin da gwamnati take so tayi wani abu takan gaiyace su ta ba su wasu ‘yan kudade don su taimaka mata wajen cim ma wannan muradin. Muna da labarin an yi taro da su an ba su kudade don su shiga kafafen yada labarai, ciki har da na sadarwa na zamani, domin su ce sune mutanan Gyallesu ko Zariya ko wani wurin, suna shan wuya a lokacin zaman Malam, domin kawai su shafa mana bakin fenti. Amma da za a je a samu mutanan unguwar ita Gyallesun na ainihi wadanda suke zaune tare da shi Malam, to da ba wannan za a ji ba. Dalili,wannan unguwa ta tattara mutane dabam-daban,misali akwai Kwalejin ilimi ta tarayya(FCE), wadda kabilu dabam-daban suna karatu a cikin wannan makaranta,akwai kuma Kwango, wadda ita ma duk a bangaren wannan unguwa take, tamkar wata ‘yar karamar Najeriya ce saboda irin al’ummar da suke zaune a wajen,wanda a da kafin zuwan Malam unguwar babu abin da ba a aiwatarwa na laifi a wajen, irin su fashi da fyade da sauransu,amma zuwan Malam abin ya tsaya baki daya. Har rikicin da aka yi a lokacin zaben 2011 nan ne kawai dokar ta-bacin da aka sanya ba ta yi amfani ba, saboda isasshen tsaro da su almajiran Malam suka bada. An cigaba da hidimomi a wajen, hasalima hatta wadansu kiristoci nan suka samu mafaka babu wanda ya taba su, karshe ma sai da suka zo daga baya suka yi wa Malam godiya. Akwai ayyuka na alheri da yawa da Malam ya rika yi a unguwar,to kuma sai a ce wai ana murna da abin da ya same shi a nan? Wannan wani yaki ne na kwakwalwa kawai aka kawo don bata suna, saboda wadancan hujjoji na tare hanya ko yunkurin kashe shugabansu duk sun ga ba su karbu ba ya sa suka bullo da wannan.
Aminiya: Ka ce ana son yin amfani da ku ne don wargaza kasa,to amma wadansu na kallon cewa ba a jinku kuna hayaniya sai idan musulmi ne ke shugabancin kasa. Me za ka ce?
Malam Yakubu A’a,ba haka ba ne. Abin da ya sanya, su wadanda ba musulmin ba ne ba su taba mu ba. Jonathon da ya taba mu ai ya ji mu. Da ya taba mu a waki’ar kudus a bara wanda ya kashe mana ‘ya’yan Malam guda 3,ai ya ji mu. Mun ta yin gangami kuma mun yi taron addu’o’i, kuma addu’o’inmu da taimakon Allah su suka kayar da Jonathan har Buhari ya zo. Wannan ma yana daga cikin abin da za a tunatar wa Buhari cewa,addu’o’inmu sun taimaka wajen zuwansa,bai kamata ya gode wa Allah da jinanenmu ba. Mun tayar wa Jonathan da addu’a kowa ya sani har sai da ya koma kamar Jaba a kasar nan, ana jifarsa,har a garinsu an jefe shi. Abacha shi ma tabamu yayi, Malam na zaune kawai bayan sallar asubahi aka zagaye gidansa da ‘yansanda daMobayil da sojoji,aka dauki Malam aka tafi da shi,shi ya sa muka yi ta mazaharori, aka yi ta bude mana wuta a Kaduna daZariya da sauran wurare. ‘Yar’aduwa da ya zo bai taba mu ba, shi ya sa ba a ji mu da shi ba. Shi ma Shema da yazo shekara 8 bai taba mu ba. Amma ka ga a Sakkwato inda Wamako ke mulki, ka ga ya taba ‘yan-uwa, ka ga an ji mu da shi. Obasanjo bai taba mu ba,hasali ma shi Obasanjo ya nuna kamar ya gamsu da abin da Malam ke yi, cewa yana da ‘yancin ya yi duk abin da yake ra’ayi, a karshe ya dauke shi wani mutum ne mai kawo zaman lafiya a kasa. Babangida ma ai ya taba mu,misali a nan Katsina a 1991 lokacin da aka diran mana ai ya ji mu. A lokacin Gwamna Barda ma da ya taba mu shi ma ya ji mu. Saboda haka wanda ya taba mu shi ke jinmu. To kuma bisa ga dukkan alamu su masu shirye-shiryen na kasashen waje suna ganin cewa shi musulmin ya fi sauki a yi aiki da shi, domin idan aka yi da wanda ba musulmin ba,to sai a ce fadan addini ne ake yi tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba, wanda wannan zai bayar da wata mahanga daban. Idan kuwa shi musulmin ne sai ya kashe mu ya murje mu, babu abin da za a yi,yamu-yamu ne, mu ci kanmu. Ka ga ke nan yaudara ce ta shigo,to mu kuma mun gane wayon, shi ya sa muke daukar wadannan matakai.
Aminiya: Ita wannan mazahara da ka nuna cewa ko addini ya bayar da damar a yi ta,to amma kuma ana kashe hanya, wanda wadansu ke ganin ana kuntata masu.
Malam Yakubu: To in dai za a yi mana adalci ba gaskiya ba ne. A nan garin (Katsina) yau kusan shekararmu 27 muna mazahara amma babu wanda ya taba kawo mana kara cewa mun kashe masa kaya ko mun tsare masa hanya. Kuma mu addini ya koya mana hakkin hanya, wanda hatta dabbobi suna da hakki a kanta. Mu mukan tafi a gefen hanya ne, muna barin sauran wuri domin sauran masu amfani da ita. Kuma muna da masu bayar da hannu masu tsara mana tarurrukanmu,akwai masu ba mota hannu da masu ba mutane hannu da sauransu. Wasu lokuttan ma ana datse jerin domin ba mutane da masu abin hawa dama su wuce. Akwai misali, a nan Katsina a wani lokaci inda muna cikin mazaharar muka zo kofar soro, a daidai lokacin kuma sarki Kabir ya dawo zai shiga gida,nan aka datse muzaharar aka ba shi hanya ya shiga gida. Shi ma wannan sarkin na yanzu hakan ta faru a kansa. Shin idan an ce ana tare hanya ne, shin mu muka fara? Wane gwamna ne ya hau kujerar mulki bai tare hanya ba,shi kanshi shugaban kasar gari sukutum yake tsaidawa. An sha yin haka. Ga masallatai ana tare hanya da coci,ga jana’iza, duk ana tare hanya,taron biki ko na siyasa duk ana tare hanya,me ya sa duk wadannan ba su zamo matsala ba sai namu? Kuma me ya sa duk duniya ake muzahara inda aka waye? Ana yi a Ingila da Amurka da sauransu, kuma ba a samun matsala, sai nan wajen? Kuma me ya sa sai tamu kawai ake samun matsala?
Aminiya: Wadannan tambayoyin da ka yi sune jama’a ke yi a kanku.
Malam Yakubu: To abin da muke kallo shi ne,su wadannan kasashen waje, idan zan fadi karara, Amurka da Isra’ila, suna da abin da suke so a Najeriya, suna da wanda ba su so. Suna son arzikin Najeriya,suna kin musulunci da musulmi. Suna ganin musulunci barazana ne ga abin da suke so su samu. To wannan kasa kasar musulmi ce, saboda kashi 80 cikin 100 na jama’ar kasar musulmi ne, don haka suna tsoron irin farkar da mutane da muke yi daga barci a kan irin yunkurinsu, ya sa suke ganinmu a matsayin masu laifi, laifin kuma namu shi ne,tayar da mutane daga barci ta hanyar wa’azoji da fadakarwa. Don me muke tayar da mutane muna cewa addini na cikin hadari? Arzikin kasa na cikin hadari?
Aminiya: To a yanzu mene ne kake ganin ya kamata a yi,daga bangarenku da kuma gwamnati?
Malam Yakubu: To mu dai a namu bangaren,muna kira ga ‘yan-uwa da muke wannan gwagwarmaya da su da su cigaba da tsayawa a bisa tsarin da muke tafiya da shi, domin dama ita wannan harka tana da tsarin da Malam ya tsara mata kuma ake tafiyar da shi,to kada a kauce wa wannan tsarin. Su saurari umarni ba ta hanyar facebook ko social media ba. Sun san yadda suke samun umarni,don haka a zama cikin natsuwa kuma a dage da addu’a. Ta sashen gwamnati kuma idan shawara za mu ba ta,to ta sani tana yin kuskure,kuma ba a gyara kuskure da kuskure. Don haka muna ba ta shawara da ta dawo cikin haiyacinta. Kuma ta sani,ko da wannan harkar ko babu ita,kasar nan za a samu canji, saboda mutane sun gaji. Ta fito fili su yarda da cewa ta yi kuskure, ba gajiyawa ba ne. Gwamnati ta gaji haka. Kuma a kafa kwamiti wanda zai zamo akwai duk wani mai ruwa da tsaki, kamar lauyoyi da mutane masu mutunci da kuma sashenmu, a ji kukan kowa don yin abin da ya dace. Sannan kuma idan suna ganinmu a matsayin matsala ce gare su,to za  su iya zama da mu. Su san yadda za su zauna da mu, sai ya zamo an yi maganin matsalar.