Ba za a yi Ittikafi da Tahajjud a masallacin Sultan Bello bana ba

A daidai lokacin da Kwamitin Gudanar da Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Kaduna ya shirya domin fara gabatar da Tafsirin bana da Shiekh Ahmad Abubakar Gumi zai fara gobe, mahukuntan masallacin sun ce a bana ba za a gudanar da Ittikafi da Tahajjud a masallacin ba.Wata takarda dauke da sanya hannun Kakakin Hukumar Masallacin […]

Ba za a yi Ittikafi da Tahajjud a masallacin Sultan Bello bana ba
Ba za a yi Ittikafi da Tahajjud a masallacin Sultan Bello bana ba

A daidai lokacin da Kwamitin Gudanar da Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Kaduna ya shirya domin fara gabatar da Tafsirin bana da Shiekh Ahmad Abubakar Gumi zai fara gobe, mahukuntan masallacin sun ce a bana ba za a gudanar da Ittikafi da Tahajjud a masallacin ba.
Wata takarda dauke da sanya hannun Kakakin Hukumar Masallacin Malam Adamu Lawal Mijinyawa da aka raba wa manema labarai a shekaranjiya Laraba a Kaduna ce ta bayyyana haka, inda ta nuna rashin jin dadin hukumar masallacin kan daukar wannan mataki tare da alkanta hakan da aikin gyaran masallacin da ake cikin yi.
“Hukumar Masallacin ta yi taro kan Tafsirin kuma ta yanke shawarar cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi zai fara Tafsirin bana ranar 6 ga Yuli (gobe) da misalin karfe 4:00 na yamma. Sai dai a yayin da muke yi wa daukacin jama’ar Musulmi fatar gudanar da azumin Ramadan cikin nasara, hukumar masallacin tana neman su gudanar da addu’o’in Allah Ya kubutar da Najeriya daga bala’o’in da take fuskantta tare da fatar Allah Ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a kowane lungu da sakon kasar nan a daukacin lokacin gudanar da azumin da bayansa,” inji sanarwar.
Sai sanarwar ta nuna rashin jin dadinta kan shawarar da ta yanke na dakatar da Tahajjud da Ittikafi a goman karshe na Ramadan. “An yanke shawarar ce sakamakon gyaran da ake gudanarwa a masallacin,” inji sanarwar.