Ba za mu amince da albashin Naira dubu 24 ba – Kungiyar Kwadago
Kungiyoyin kwadago sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin da Gwamnatin Tarayya ta gabatar na biyan Naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikta. A shekaranjiya Laraba ce Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya shaida wa manema labarai cewa bayan tattaunawa da gwamnatocin jihohi, Gwamnatin Tarayya za ta amince da Naira dubu 24 a […]
Kungiyoyin kwadago sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin da Gwamnatin Tarayya ta gabatar na biyan Naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikta.
A shekaranjiya Laraba ce Ministan Kwadago, Chris Ngige, ya shaida wa manema labarai cewa bayan tattaunawa da gwamnatocin jihohi, Gwamnatin Tarayya za ta amince da Naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata duk da cewa ba ta kai ga cimma matsaya ba.
Hakan na zuwa ne bayan da aka koma teburin tattaunawa a tsakanin gwamnatin da kungiyoyin kwadagon, wadanda suka yi yajin aikin gargadi mako biyu da suka gabata.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito Sakataren Tsare-Tsare na Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Kasa (ULC), Kwamared Nasir Kabir yana cewa, ana su bangaren sun dauki matakin da gwamanatin ta dauka game da mafi karancin albashin a matsayin wasan yara.
Don haka ba za su taba amincewa da wannan kudi ba, domin tun farko ba haka suka yi da gwamnati ba.
Sakataren ya ce, idan har gwammnati ta gaza biya musu bukata a kan albashin, to akwai matakan da za su dauka da suka hada da sake tafiya yajin aiki, kuma duk inda suka san akwai ma’aikatansu a ko’ina a fadin kasar nan, to za su janye su daga wurin.
Nasir ya kara da cewa “Ya kamata fa gwamnati ta sani cewa, idan aka ce babu ma’aikaci to babu gwamnatin ma kanta, don haka ma’aikata su ne gatan gwamnatin. Da farko mun cimma matsaya da jami’an gwamnati inda aka roki kungiyoyinmu na kwadago kan mu hakura da mafi karancin albashi ya koma Naira dubu 30, to amma su ba su amince da haka ba ma.”
“Ya kamata fa gwamnati ta sani cewa kananan ma’aikata na cikin kunci da wahala, don haka idan aka ce za a yi karin da bai taka kara ya karya ba me aka yi ke nan? Gidan jiya ce za a koma kawai. Don haka matukar gwamnati ba ta saurari koke-koken talakawa da kananan ma’aikata ba, to insha Allahu za mu yi wa gwamnati yaren da take so, na janye ma’aikatanmu daga ma’aikatun gwamnati,” inji shi.