Ba za mu bar ’yan kasashen waje su yi zaben bana ba – Mkanu
Shugaban Hukumar Shigi da Fice (NIS) Mista Ubi Mkanu ya ce ba za a bar baki ’yan kasashen waje su jefa kuri’a a zaben bana ba. Shugaban Hukumar ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da manema labarai, a Yola, inda ya ce “Hukumarmu na iya kokarinta domin tabbatar da rashin halartar bakin da […]
Shugaban Hukumar Shigi da Fice (NIS) Mista Ubi Mkanu ya ce ba za a bar baki ’yan kasashen waje su jefa kuri’a a zaben bana ba.
Shugaban Hukumar ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da manema labarai, a Yola, inda ya ce “Hukumarmu na iya kokarinta domin tabbatar da rashin halartar bakin da ba ’yan kasa ba rumfunan zabe ban aba.”
Ya ce hukumarsu na kokari wajen tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya inda ya ce za su sallami duk wanda suka kama ya bar baki sun yi zabe a bana.
Ya ce kalubalen da za su fuskanta a wannan aiki shi ne kasancewar tashin hankali da Arewa maso Gabas ke fuskanta ciki har da Jihar Adamawa na hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa.
Ya bukaci mutanen unguwani da kauyukan da ke kan iyaka su tallafa wa ma’aikatansa wajen aikin tsaro, wajen kai rahoton wanda ba dan kasa ba ko wanda ake da shakku kan take-takensa.
Ya jinjina wa al’ummar jihar Adamawa kan yadda suka karbi sabon fasfot, inda ya ce akalla mutum dubu biyar daga jihar sun yi sabon fasfot a bara.