Ba za mu cire hannunmu a aikin hajji ba – Sarkin Saudiyya

A ranar Litinin ne Sarkin Salman na Saudiyya ya ce ba za ta cire hannunta daga shirya aikin hajji ba, biyo bayan turmutsitsin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mahajjata.Har ila yau,ya ce wannan zance ne na rashin sanin ya kamata, sannan maganar cewa kasar Saudiyya ba za ta iya kula da mahajjata ba, ba […]

Ba za mu cire hannunmu a aikin hajji ba – Sarkin Saudiyya
Ba za mu cire hannunmu a aikin hajji ba – Sarkin Saudiyya

A ranar Litinin ne Sarkin Salman na Saudiyya ya ce ba za ta cire hannunta daga shirya aikin hajji ba, biyo bayan turmutsitsin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mahajjata.
Har ila yau,ya ce wannan zance ne na rashin sanin ya kamata, sannan maganar cewa kasar Saudiyya ba za ta iya kula da mahajjata ba, ba zai shafi tsara hajjin shekara-shaekarar da kasarsa take yi ba.
Hadarin dai ya faru ne a ranar 24 ga Satumbar da ya gabata a lokacin da wasu sahun mahajjata suka hade da juna a wajen jifan shedan. Gwamnatin Saudiyya ta ba da sanarwar mutuwar mutane 769.
Kodayake, kamfanin dillancin labarai na AP ya ce, mutane 1,480 ne suka hallaka a lokacin, wanda idan hakan ya tabbata  zai zama hadarin aikin hajji da ya fi kowanne haifar da mutuwar alhazai a shekaru masu yawa.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya zargi Saudiyya da gazawa wajen tsara aikin hajji da kuma rashin cancantarta, a yayin Jagoran Addini na Iran ya ce, ya kamata kasashen Musulmi su fara daukar nauyin tsara aikin hajjin.
’Yan Iran su 465 ne suka mutu a Makka a yayin da Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fidda sanarwa a jiya cewa alhazanta guda 181 ne suka mutu, sannan guda 53 sun bace.
A watan jiya ne dai Sarkin ya bukaci a ba shi rahoton yadda ake tsara aikin hajjin.