Ba za mu daina tattaki ba – Kungiyar Shi’a
Aminiya ta zanta da shugaban Gidauniyar kula da marayu ta kungiyar ’Yan Uwa Musulmi Ta Najeriya wato ’yan Shi’a, Malam Abdulhamid Bello, inda ya yi bayani a kan dalilin dogewa da tattakinsu na shekara-shekara. Haka nan ya yi bayani a kan wasu batutuwa, ciki har da na alakarsu da Kirista Wane abu kuke so […]
Shaikh (Dokta) Ahmad Gumi
Aminiya ta zanta da shugaban Gidauniyar kula da marayu ta kungiyar ’Yan Uwa Musulmi Ta Najeriya wato ’yan Shi’a, Malam Abdulhamid Bello, inda ya yi bayani a kan dalilin dogewa da tattakinsu na shekara-shekara. Haka nan ya yi bayani a kan wasu batutuwa, ciki har da na alakarsu da Kirista
Wane abu kuke so ku cin ma wa da wannan muzahara da kuka yi a Abuja da ta kai ga fuskantar rasa rayuka?
Koda ake kiranta Muzahara, wannan ba Muzahara ba ce. Mu a wajenmu a na kiran shi da “Tattakin Arba’un.” Manufarsa shi ne mu tunatar da kawunanmu irin wahalhalun da iyalan gidan Manzon Allah (Saw) suka sha na tattakawa, da aka tilasta masu yi bayan Waki’ar Karbala da ke kasar Iraki a shekara ta 61 a filin Karbala, inda suka tattaka daga Karbala har zuwa Kufa sannan Sham. To wannan al’amari ne muke rayawa kuma ba a wannan nahiyar tamu ce kadai ake yi ba, al’amari ne da ke wakana a kasashen duniya daban-daban.
Kamar daga wadanne yankuna ne ake halartar wannan tattaki na Abuja?
A gaskiya ba zan iya kididdige alkaluman ba saboda ba rajistar jama’a ake yi ba. Sai dai abu guda da na sani, duk wani mai shaukin imani na halartan wannan gangamin. Shi ya sa kake ganin al’ummar da suka halarta suna da yawa. Idan za a koma baya lokacin da ake yin wannan tattaki a Zariya kafin waki’ar da ta auku a baya, za ka ga cewa miliyoyn jama’a ne ke halarta da zai yi wuya a lissafa. An dauki shekaru da dama ana yi ba tare da an taba fuskantar wata matsala ba duk da cewa har daga makwabtanmu kamar Jamuhuriyar Kamaru da Nijar duk ana zuwa a lokacin yinsa, kuma ko wannan din ma akwai ’yan uwa daga bangarori daban-daban da suka halarta.
Kuma sai ga shi ana samun arangama a tsakanin jami’an tsaro da kuma ku, me ya sanya?
To, mu dai wannan kalmominku ne na ’yan jarida da kuke bayyana abin da ake yi mana a matsayin arangama ba mu gane shi ba. Ai ana arangama ne idan ta kai ga an yi fito-na-fito, ni na zo da zimmar za mu yi fada, kai ma ka zo da zimmar hakan, sai mu yi arangama. To, mu ba ma arangama. Na ba ka misali da abin da ya faru a ranar Asabar, ranar farko da aka fara wannan tattaki da ya faru a garin Zuba. Amma idan aka zalunci mutum ko aka buge shi ya rama, to wannan dama dabi’a ce ta dan Adam ba yadda za ka tura mutum har bango sannan ka yi tsammanin ba zai mayar da martani ba.
Kun tsara za ku yi kwana 4 a wannan tattakin sai ga wannan ibtila’in, ko abin da ya faru zai sa ku hakura da ragowar yini na karshen?
Shin yanzu idan aka kashe dan uwanka a kan yin Sallah, kai za ka daina? Idan da kama ka aka yi, aka hana ka, to wannan wani abu daban ne. Mun san ai Aikin Hajji wajibi ne ko, kuma an ba da dama idan aka hana ka ka hakura ka yi “talili” ka koma, wannan ayar Kur’ani ce, haka kuma idan ziyara ce. Amma idan an hana ka yin Sallah aka kunkume ka, sai ka aiwatar da Sallar koda ta hanyar kamantawa ne a zuciya. Ba kuma ina nufin hada wannan al’amari ba ne da matsayin Sallah ba, saboda ai Sallah wajiba ce. Sai dai tun da shi ma alama ce ta raya addini, to a wajenmu shi kansa addinin ne kuma imani ne. Ba mu zalunci kowa ba, kuma ba za mu daina ba. Ba kuma wanda ya isa ya hana mu. Saboda idan har muka yarda muka hanu muka daina, to a wata rana abin da ke matsayin wajibin ma sai an hana mu.
An kama wasu annabawa an tsare, haka nan wasu shugabanni a kan gaskiyarsu. Shin me zai hana ku ma ku hakura da wannan zanga-zangar da kuke yi na sai an saki malaminku, wanda ke kai wa ga rasa mabiyanku a wani lokacin?
Wa ya gaya maka wadanda aka kaman mabiyansu sun hakura sun yi shiru, ko al’ummar annabawan da aka tsaren sun yi shiru sun ce shi ke nan a je a kashe su? Ai idan mun yi shiru mun yi watsi da jagoranmu ke nan baki daya, kuma mun yi watsi da addinin da yake shiryatar da mu a kai. Saboda haka wannan abin da muke yi shi ne abin da magabata suka dore a kai, haka nan kuma mu ma za mu yi ko yana raye ko ba ya raye.
Wasu na zargin cewa alakarku da mabiya addinin Kirista na neman ta zarce wadda kuke da ita da Musulmi, har ake cewa kun ma fi kusa da su. Me za ka ce game da wannan?
Wannan alaka ce ta mutuntaka da ta samo asali a sakamakon rigingimu da ake samu a tsakanin al’ummar Musulmi da kuma su Kirista, wadda ke neman a fahimci juna. Muna taimaka masu a matsayinsu na mutane kamar yadda addini ya nuna a kaunaci dukkan dan Adam ko da mara addini ne, ba kamar yadda wasu ke tunani ba.