Ba za mu iya biyan bukatun malaman jami’o’i ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wadatattun kudaden da za ta iya biya wa malaman jami’o’in kasar nan bukatunsa da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta nemi a biya kafin ta tsunduma yajin aiki. Ministan Ilmi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a […]

Ba za mu iya biyan bukatun malaman jami’o’i ba – Gwamnatin Tarayya

Shugaban kasar kamaru, Paul Biya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wadatattun kudaden da za ta iya biya wa malaman jami’o’in kasar nan bukatunsa da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta nemi a biya kafin ta tsunduma yajin aiki.

Ministan Ilmi, Adamu Adamu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata a Abuja. Ya ce faduwar farashin man fetur a duniya ya shafi kudaden shiga da kuma ribar da kasar nan ke samu.

Ya ce wannan faduwar darajar farashin man fetur ya shafi kowane fanni na tattalin arzikin kasa, har ma da bangaren ilmi. Haka kuma gwamnatin tarayya ta zargi gwamnatin Umaru ‘Yar’Adua, domin a lokacin ta ne ta yi wa malaman jami’o’i alkawura masu karfi a lokacin farashin danyen man fetur na da tsada a kasuwannin duniya sosai.

Adamu ya ce yajin aikin da ake faman kiki-kaka a yanzu, ya samo asali ne tun lokacin gwamnatin Umaru ‘Yar’Adua, wadda a lokacin gwamnati ta sa hannun yarjejeniya da ASUU dangane da batun rika daukar nauyin dukkan kudaden da jami’o’in gwamnati za su rika kashewa.

Minista Adamu ya ce yarjejeniyar da aka kulla a lokacin, an amince gwamnatin tarayya za ta rika kashe wa jami’o’i har naira tiriliyan 1.3 cikin kowane watanni shida. A wancan lokacin kuwa inji Adamu, Najeriya na matukar samun kudaden shiga masu yawa, saboda farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya, ya yi tashin gwauron-zabo.

Daga nan sai ministan ya roki iyayen dalibai, malamai da su ma daliban da su rika sara su na duban bakin gatari, idan ana batun neman biyan bukatu daga hannun gwamnatin tarayya.

Ya ce kamata ya yi a rika yin la’akari da cewa akwai sauran fannoni masu yawa da su ma ke bukatar gwamnati ta rika daukar nauyin gudanar da tafiyar da su.