Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba — Gwamnoni

Ba zai yiwu a ɗora mana nauyin da ba za mu iya saukewa ba.

Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba — Gwamnoni

Taron Kungiyar Gwamnoni Arewa. (Hoto: NAN)

Gwamnoni 36 na Nijeriya sun yi fatali da Naira 60,000 da Gwamnatin Tarayya a bayan nan ta miƙa tayi a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Gwamnonin sun ce jimillar wannan kuɗin ya wuce misalin da zai zame musu nauyin da ba za su iya saukewa ba.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Darektar Sadarwa da Hulɗa da Jama’a ta Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed ta fitar a wannan Juma’ar.

Sanarwar ta ambato ƙungiyar gwamnonin na cewa ko da an ƙayyade Naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, ba za su iya biyan ma’aikatan jihohinsu ba domin ba abu ba ne da zai ɗore.

Gwamnonin sun bayyana cewa muddin aka ayyana Naira 60,000 ɗin a matsayin mafi ƙarancin albashi, za a kai ƙadamin da sai sun fita neman rance domin biyan ma’aikatan jihohinsu albashi.

“Kenan hakan na nufin da yawa daga cikin jihohin za su riƙa kashe duka kuɗin kason da suke samu daga Gwamnatin Tarayya wajen biyan albashin ma’aikata, ba tare da komai ya ragu ba don gudanar da wasu ayyuka,” in ji sanarwar.

Kazalika, gwamnonin sun buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da ke ci gaba da kai ruwa rana kan tsayar da mafi ƙarancin albashi musamman ’yan kwadago da su yi taka-tsan-tsan tare da la’akari da tasirin hakan duba da yanayin tattalin arzikin ƙasar.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne dai Ƙungiyoyin Ƙwadago na Nijeriya da suka haɗa da NLC da TUC suka tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani yayin da Gwamnatin Tarayya ta miƙa musu tayin Naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ma’aikata.

Sai dai daga bisani bayan kwanaki biyu ƙungiyoyin ƙwadagon sun mayar da wuƙarsu cikin kube tare da komawa kan teburin sulhu da gwamnati domin ci gaba da tattaunawa da samar da matsaya kan mafi ƙarancin albashin ma’aikatan.

Wannan dai ya biyo bayan alƙawarin da Gwamnatin Tarayyar ta yi na ƙara wani adadi kan tayin Naira 60,000 da ta miƙa musu da farko.