Ba za mu iya ciyar da kasar nan da shinkafa ba har sai… – Bala Faru
“Matukar ana son kasar nan ta fita daga yin dogaro da shinkafar kasashen waje, to dole ne a gyara lamarin ta hanyar cire wadanda ba manoman gaskiya ba”. Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin tsohon shugaban ‘yan kasuwa, sannan sanannen manomi a Jihar Sakkwato, Alhaji Bala a makon da ya gabata lokacin da wakilinmu […]
“Matukar ana son kasar nan ta fita daga yin dogaro da shinkafar kasashen waje, to dole ne a gyara lamarin ta hanyar cire wadanda ba manoman gaskiya ba”.
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin tsohon shugaban ‘yan kasuwa, sannan sanannen manomi a Jihar Sakkwato, Alhaji Bala a makon da ya gabata lokacin da wakilinmu ya ziyarci ofishinsa dake cikin Kasuwar Kara a Sakkwato. “Ba za mu iya ciyar da kasar nan da shinkafa ba matukar ba a cire manoman riga da baki da biro cikin na gaskiya ba, don na san wahalar da muke sha sama da shekara 15 ina noman shinkafa da alkama da karas da tumatir da sauransu.
“A duk lokacin da aka fito da wani shirin taimakon manomi zaka gan shi abin sha’awa amma da zaran an soma sai ka nemi tasirin abin ka rasa, a kungiyarmu ta noma sananna ce dake da mambobi 340 a shirin taimakon manoma na Jihar Sakkwato, an ba mu injinan ban ruwa 20 mu raba ni na samu inji daya, ina noma ket bakwai biyar a karamar Hukumar Rabah biyu a Dundaye, to fada min yadda injin daya zai taimaki nomana, bayan ba a bani taki da tallafin kudi ba, a kowace rana sai na sayi litar man fetur 15 don yin ban ruwa a gona, injin biyar nake amfani da shi masu aiki na ba su 3,000 a kullum, dubi wannan amma aka kasa bamu ko irin da zamu shuka sananan a yi tunanin ciyar da kasa da abinci? Gaskiya da sake” cewar Alhaji Bala.
Ya kara da cewar shirin anko bai maganarsa ma sam, domin an sanya sun bude asusun ajiya a Jaiz da sitalin da first dukkansu har yanzu shiru ba wani tallafi da suka amfana kan haka yake kira ga gwamnati ta duba abin da take fitarwa baya isa ga nanoma, a yi gyara domin wasu ma shugabannin kungiyoyin manoma sun mayar da kungiyar sana’a, suna fitowa da shirye-shiryen da gwamnati ba ta san da su ba, ana karbar kudin manoma masu yawa da sunan zai karbi tallafi.
“Gwamnati ta waiwayi kungiyoyin na kwalkwalawa guda 17 kowace tana da mamba 20, ba sai in za a ba da tallafi su ga mutane na zuwa gonarsu suna daukar hota da zimmar wai ta masu hoton ce su karbi tallafi su bar masu aikin da gaske a yanzu manomi ya gaji da alkawali don ba a cika masa. Gwamnatin Sakkwato ta yi kokarin sayar da buhun taki naira dubu hudu injin dubu 25 abin tinkaho ne sai dai ta kula ‘yan siyasa da boko ne suka mamaye tallafin wasu manoma sun fara kasawa ba kudi sha’awa ce kawai ga kuma hasara da aka samu a wannan shekara ruwa na kasa ba su zo wasu wurare ba,” in ji tsohon shugaban ‘yan kasuwan.
Da ya juya kan yadda za a rage tsadar abinci ya ce a watan 9 na kowace shekara abinci ke fara shiga kasuwa har zuwa watan biyun wata shekara, ya kamata gwamnati ta samu wasu amintattunta ta ba su kudi su sayi abincin a ajiye, in katse ya fara tsada a rika saidawa talakawa da arha, a 2017 an fara sayen buhun abinci kan dubu 9 amma kafin shekara ta kare ya koma dubu 20, noman Sakkwato baya isar ta kadai a kowane mako sai an shigo da gero mota 10 masara 6 daga Fatiskum, Dawa kuma biyar zuwa 10 a Dandume da sauran wurare, shinkafa ma haka ya kamata a duba gwamnati ta shigo da gaske don magance abinci ga talakawa masu sayarwa ma na fuskantar karancin ciniki, baki sun rage zuwa duk mai buhu 100 yanzu ba shi da jarin buhu 20, a cewarsa.