Ba za mu iya tsige Tambuwal daga kujerarsa ba – PDP
Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan ta ce ba za ta iya tsige Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal daga kan kujerarsa ba, bayan komawarsa jam’iyyar adawa ta APC a ranar Talatar da ta gabata. Jam’iyyar PDP ta ce, zai yi wuya ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku na wakilan majalisar da ake […]
Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar nan ta ce ba za ta iya tsige Shugaban Majalisar Tarayya Alhaji Aminu Waziri Tambuwal daga kan kujerarsa ba, bayan komawarsa jam’iyyar adawa ta APC a ranar Talatar da ta gabata.
Jam’iyyar PDP ta ce, zai yi wuya ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku na wakilan majalisar da ake bukata domin tsige Tambuwal daga kujerar shugabancin majalisar kamar yadda jaridar Premium Times ta intanet ta ruwaito.
Kafin a tsige shugaban majalisar daga kujerarsa, tilas ne a samu amincewar wakilai 240 daga cikin wakilai 360 na majalisar, kuma a yanzu Jam’iyyar PDP na da wakilai 189 ne a majalisar yayin da Jam’iyyar APC ke da 159, sai sauran 12 suka fito daga sauran kananan jam’iyyun adawa.
Da yake magana kan batun tsigewar Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Leo Ogor ya ce, “Ina jin akwai bukatar mu tuna da tsarin mulki. A cewar tsarin mulki, sai ka samu rinjayen kashi biyu bisa uku kafin ka tsige shugaban majalisa. Shin muna da kashi biyu bisa uku? Wannan wani batu ne da ya kamata mu lura da shi.”
Ya ce, “Mu jira hukuncin kotu kan lamarin. Kuma ina jin wannan ne babbar dama gare mu, mu yi kira ga sashin shari’a, shi ma bangare ne na gwamnati – domin jinkirta yin adalci kamar hana adalcin ne. Wannan batu da ke gabansu, wajibi ne su yanke hukuncin da ya dace ta yadda za a huta da batun canja shekar.”
Ya ce PDP za ta rika sanya ido kan Tambuwal ta ga yadda zai rika jagorantar majalisar.
A dauki watanni ana rade-radin cewa Tambuwal zai koma Jam’iyyar APC, a makon jiya ya halarci wani taro na APC a jiharsa ta Sakkwato lamarin da ya kara rura wutar jita-jitar zai bar PDP. Lokacin da Aminiya ta tuntubi kakakinsa Imam Imam a makon jiya, Tambuwal ya bayyana cewa zai bayyana matsayinsa nan ba da jimawa ba, sai ga shi a ranar Talata ya kawo karshen jita-jitar ta hanyar bayyana wa ’yan majalisar cewa: “Kafin mu dage zama, ina da sanarwa ga wannan majalisa. Kamar yadda tsarin mulkin 1999 ya tanada da kuma lura da abubuwan da suke faruwa a PDP a jihata, Jihar Sakkwato, ina sanar da komawata Jam’iyyar APC.”
Majalisar ta dage zamanta zuwa 3 ga Disamba, matakin da wasu suka fassara da dakile yunkurin da PDP za ta yi domin musguna masa. Sai dai shugabannin Jam’iyyar APC a majalisar sun ce an dage zamanta ne domin ba wakilai damar nazari kan kasafin kudin badi.
Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP na kasa (NWC) ya gana da shugabannin jam’iyyar a majalisar wakilai a kan sauya shekar, kuma bayan nazari a kan al’amarin ya bukaci shugaban ya nuna dattako ya sauka daga mukaminsa tun da sabuwar jam’iyyarsa ce marar rinjaye a majalisar.
Wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jam’iyyar Oliseh Metuh ya fitar, ta ce kamata ya yi shugaban majalisar a matsayinsa na zababben jami’i mai dattako, ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa tunda ya fice daga cikin jam’iyya mai rinjaye a majalisar.
Tambuwal ya zama shugaban majalisar na biyu da ya fito daga jam’iyya marar rinjaye, inda a Jamhuriyya ta Biyu Edwen Ume-Ezeoke na Jam’iyyar NPP ya shugabanci majalisar mai rinjayen Jam’iyyar NPN a wata kawance da jam’iyyun biyu suka kulla.