Ba za mu janye dokar hana dalibai mata sanya abaya a makarantu ba — Faransa

Makarantun kasarmu babu ruwansu da addini.

Ba za mu janye dokar hana dalibai mata sanya abaya a makarantu ba — Faransa

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine. (Hoto: Sergei SUPINSKY / AFP)

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce gwamnatinsa ba za ta fasa aniyarta ta haramta wa dalibai mata sanya abaya a makarantu ba.

A jiya Juma’a ce Macron ya ziyarci wata makarantar sakandare a garin Orange da ke Kudancin Faransa, inda ya yi tsokaci game da haramta sanya abaya da kasar ta yi.

“Makarantun kasarmu babu ruwansu da addini, kuma karatu kyauta ne sannan dole ne … duk wata alamar addini ba ta da gurbi a nan,” in ji Macron, a cewar gidan talabijin na BFMTV.

Shugaban kasar ya goyi bayan matsayin da Ministan Ilimi Gabriel Attal ya dauka, yana mai cewa: “Ba za mu sauya wannan matsayi ba … Za mu tabbatar mun aiwatar da shirin.”

Macron ya ce za a tura ma’aikata don goyon bayan shugabannin makarantun da ake fuskantar kalubale wajen aiwatar da dokar, sannan za a kafa wani kwamiti na tattaunawa da dalibai da iyayensu.

“Ba za mu bar komai ya wuce ba tare da daukar mataki ba,” in ji shugaban kasar.

Attal ya sanar cewa daga ranar Litinin ba za a bari daliban da ke sanya abaya su shiga aji ba, lokacin da za a dawo daga hutu.

“Za mu yi wa dalibai maraba da dawowa makaranta kuma za a tattauna domin fahimtar da su dalilan yin wannan doka da kuma abin da ya sa ba za mu bari a rika sanya abaya a makarantu ba,” a cewar Attal.

Gwamnatin Faransa tana shan suka bisa shimfida dokoki masu musguna wa Musulmai ciki har da dokar kai samame masallatai da cibiyoyin Musulunci.