Ba za mu karɓo bashin ketare don cike gibin Kasafin Kudin 2024 ba — Ministan Kudi

Ministan ya ce karbar bashin ketare ya kai matakin da kasashe irin Najeriya ba za su iya dauka ba.

Ba za mu karɓo bashin ketare don cike gibin Kasafin Kudin 2024 ba — Ministan Kudi

Ministan Kudi Mista Wale Edun, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta yi duk mai yiwuwa na kaucewa ranto kudi daga ketare da zummar cike gibin Kasafin Kudin 2024.

Ya ce maimakon haka, za a samar da kudin shiga mai yawa, da za a yi amfani da su wajen samar da Kasafin Kudin baɗi.

Mista Edun ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa da ke binciken tsarin kashe kudin gwamnati na matsakaicin zango, daga shekarar 2024 zuwa 2026, da Sanata Sani Musa ke jagoranta.

Mista Edun ya bayar da misali da kasashen da suka ci gaba, da ya ce suna kara kudin ruwa domin sauko da hauhawar farashin kayayyaki, da hakan ke taimaka wa tattalin arzikin su.

Da yake wannan furuci a gaban shugabannin Hukumar Tattara Haraji da Hukumar Kula da Bashi ta Kasa, Ministan ya ce karbar bashin kasashen ketare ya kai matakin da kasashe irin Najeriya ba za su iya dauka ba.

“A yanayin da muke yanzu muna da kwantan bashi, saboda haka tsarin da muke yi shi ne dogaro da kudin haraji,” inji Ministan.

Sai dai kuma shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa, ya nuna shakku kan yadda ya ga kudin shiga da na haraji da hukumomi da ma’aikatu suka ce za su samar a 2024, yana mai cewa bai kai wanda Ma’aikatar Kudi ta ce za ta yi amfani da su a kasafin kudin badi ba.

Sanata Sani ya kara da cewa, “ya kamata ofishin Akanta-Janar ya bincike dalilin da wasu hukumomi da ma’aikatu ba su tura kudin da ake tarawa a asusun Gwamnatin Tarayya, wanda hakan yana buɗe kofar yin sama da fadi da arzikin kasa.”