Ba za mu kara farashin kaya a Ramadan ba —’Yan kasuwan Kano

’Yan kasuwa a Jihar Kano musamman masu sayar da kayan abinci a Kasuwar Hatsi ta Dawanau da kuma Kasuwar Singa sun bayar da tabbacin cewa ba za a samu hauhawar kayan masarufi a azumin bana ba, kamar yadda ya sha faruwa a shekarun baya. Aminiya ta samu tabbacin hakan ne ta bakin Shugaban Kasuwar Hatsi […]

Ba za mu kara farashin kaya a Ramadan ba —’Yan kasuwan Kano

Kayan abinci

’Yan kasuwa a Jihar Kano musamman masu sayar da kayan abinci a Kasuwar Hatsi ta Dawanau da kuma Kasuwar Singa sun bayar da tabbacin cewa ba za a samu hauhawar kayan masarufi a azumin bana ba, kamar yadda ya sha faruwa a shekarun baya.

Aminiya ta samu tabbacin hakan ne ta bakin Shugaban Kasuwar Hatsi ta Dawanau, Alhaji Sani Ahmad da takwaransa na Kasuwar Singa, Alhaji Uba Zubairu Yakasai, yayin ziyarar jan kunne da Hukumar Yaki da Cin hanci ta Jihar Kano ta kai kasuwannin.

Tun da farko Hukumar ta bakin Shugabanta, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ta ce ta kai ziyarar ce bisa rade-radin da take samu cewa wasu ’yan kasuwa sun fara yunkurin karin farashin kayan abinci musamman ma gero da wake saboda gabatowar watan azumi.

Haka kuma a cewar Hukumar, ta sami rahoton cewa wadanda ake zargin suna shirin boye kayayyakin ne da gangan domin kawai su ci kazamar riba a lokacin azumi.

Sai dai da yake jawabi, Shugaban kasuwar Dawanau, Alhaji Sani Ahmad ya ce ko kadan ba su da shirin yin kari a kayayyakin abinci da suke da su.

A cewarsa, kungiyarsu na zagayawa loko da sako na kasuwar domin ganin an tababatar da adalci tsakanin ’yan kasuwa don haka ne ma ya bukaci al’umma da ta kwantar da hankali cewa batun karin farashin kayayyakin abinci babu shi.

Shi ma da yake bayar da nasa tabbacin, Shugaban Kasuwar Singa, Alhaji Uba Zubairu ya ce babu batun karin farashin kayan abinci a kasuwar, musamamn ma sukari da madara da al’umma suka fi amfani da su a lokacin na azumi.
Ya ce galibin ’yan kasuwa suna da kayayyakin da za su ishi al’umma har a gama azumi ba tare da an shiga halin ni ’yasu ba.

Da yake jawabi tun da farko, Shuagaban Hukumar, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce ya ziyarci kasuwar ne domin ba su girmansu ba wai don barazana ba.

Ya kuma nemi shugabannin da su ja kunnen mabiyansu da su kauce wa jefa jama’a cikin kunci ba tare da wani dalili ba.

Sannan ya sha alwashin kwace kayan duk wanda aka kama da boye kayan abinci da gangan domin musgunawa al’umma.

“Wannan karon duk wanda muka kama da boye kayan abinci to za mu kwace mu kuma raba kayan ga mabukata kamar yadda doka ta tanada.

“Ba za mu mayar wa da mutum kamar yadda muka yi a baya ba,” inji shi.