‘Ba za mu kwata irin murdiyar ku ba’ – APC ga Gwamnonin PDP

Mai rikon mukamin Sakataren Yada Labarai na kasa a Jam’iyyar APC, Kwamared Timi Frank, ya caccaki kungiyar gwamnonin PDP, game da zargin da suka yi cewa akwai shirin yin katunan zaben bogi da jami’an tsaro na bogi, wadanda za a yi amfani da su don murda zaben Gwamnan Jihar Bayelsa.Kwamared Timi ya bayyana wa jaridar […]

‘Ba za mu kwata irin murdiyar ku ba’ – APC ga Gwamnonin PDP
‘Ba za mu kwata irin murdiyar ku ba’ – APC ga Gwamnonin PDP

Mai rikon mukamin Sakataren Yada Labarai na kasa a Jam’iyyar APC, Kwamared Timi Frank, ya caccaki kungiyar gwamnonin PDP, game da zargin da suka yi cewa akwai shirin yin katunan zaben bogi da jami’an tsaro na bogi, wadanda za a yi amfani da su don murda zaben Gwamnan Jihar Bayelsa.
Kwamared Timi ya bayyana wa jaridar Dailytrust cewa, Shugaba Muhajmmadu Buhari ba zai taba yarda a yi amfani da sojoji a rumfunan zabe ba, saboda ya jajirce wajen nuna kaunarsa ga kafuwar dimokuradiyya.
A cewarsa: “Jam’iyyar APC, kamar yadda aka sani jam’iyya ce ta wadanda suka san abin da suke yi tun tashin farko. Don haka ne ma ’yan Najeriya suka samu kwarin gwiwa har suka zabeta. Ina mai tabbacin cewa, babu yadda za a yi APC ta yarda da kowace irin murdiyyar zabe. Bisa la’akari da karfin mu da kimar mutumtakar ’ya’yan jam’iyyar APC, ba mu da hannu wajen murde kowane irin zabe a Najeriya
“A kowane irin yanayi, za mu ci zabe ne kawai, gwargwadon karbuwarmu ga jama’a. Shugaban da muke da shi a yau ba zai amince da kowane irin rashin adalci ba ko keta haddi daga kowane rukuni na al’umma.
“Don haka, ina mai sanar da ku cewa, ba tare da tsoro ko alfarma ba, Shugaba Buhari ba zai kyale jam’iyya ko ’ya’yanta ko sojoji a yi amfani da su wajen zabe ba, saboda shi mai fafutikar kafuwar dimokuradiyya ne na gaskiya. Yana kaunar dimokuradiyya.
“Saboda haka mun tabbatar da cewa, abin da gwamnonin jam’iyyar PDP ke fada na daga cikin manufofin su. Wadannan irie-iren abubuwan da suke aikatawa, a lokacin da jam’iyyar su ke rike mulki. Shi ya sa suke kokarin cusa irin wannan tunanin a kwakwalen ’yan Najeriya. Jam’iyyar APC na iya bakin kokarinta don ganin ta ci zabe a Jihar Bayelsa, amma ba ta hanyar murdiyya ba.”