Ba za mu nemi afuwar Buhari ba – PDP
Shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa sun ce suna na kan bayanin da suka yi cewa wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC suna taimaka wa mahara ta hanyar sakin bakinsu ba linzami.Jam’iyyar PDP ta kuma zargi APC ta zafafa harkokin siyasa a yunkurinta na neman mulki ta hanyar kawar da hankalin Shugaba Goodluck Jonathan daga shirinsa na sake […]
Shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa sun ce suna na kan bayanin da suka yi cewa wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC suna taimaka wa mahara ta hanyar sakin bakinsu ba linzami.
Jam’iyyar PDP ta kuma zargi APC ta zafafa harkokin siyasa a yunkurinta na neman mulki ta hanyar kawar da hankalin Shugaba Goodluck Jonathan daga shirinsa na sake fasalin kasar nan.
Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PDP ta kasa Olisa Metuh ne ya bayyana haka a hedkwatar jam’iyyar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce abin da APC za ta iya gabatarwa shi ne cin fuskar kujerar Shugaban kasa da shugabannin PDP na kasa, amma ba neman kawo kyakkyawan shugabanci na gaskiya ba.
“Batun sukar da ta shafi bayanin da muka fitar bayan harin bam din Nyanya, musamman kan bayanai da kalaman shugabannin APC kamar Buhari da sauransu, wannan bayani an yi shi, kuma dukkan ’yan kwamitin gudanarwar PDP sun amince da shi; kuma dukansu sun yi ittifaki a kansa. Muna nan kan matsayinmu, yau ma muna kan matsayinmu domin da shugabannin ’yan adawa suna taka-tsantsan wajen kalamansu, ba za a zafafaf harkokin siyasa ba.”
Ya kara da cewa, “Batun shi ne wasu daga cikin maharan suna samun tallafin kudi ne daga mutanen da irin wadancan kalamai na shugabannin ’yan adawa ke karfafa musu gwiwa. Muna murna a yau, sun zabi hanyar hikima wajen bayyana ra’ayinsu.”
Tunda farko shugaban kungiyoyin sakatarorin watsa labarai na PDP na shiyya-shiyya, Mista Ali Odefa ya bukaci ’yan adawa su rika yin suka mai ma’ana kuma su hada hannu da PDP wajen gina Najeriya.