Ba za mu raga wa wanda ya karya doka ba – Afakallah
Daga dukkan alamu an sake sanya zare a tsakanin Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano da ’yan fim na bayan kama fitaccen Darkata Sanusi Oscar 442 da hukumar ta yi. Hukumar wadda ta gurfanar da Oscar a kotu, ta tuhume shi da laifin fitar da waka ba tare da hukumar ta tace ba, amma a […]
Daga dukkan alamu an sake sanya zare a tsakanin Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano da ’yan fim na bayan kama fitaccen Darkata Sanusi Oscar 442 da hukumar ta yi. Hukumar wadda ta gurfanar da Oscar a kotu, ta tuhume shi da laifin fitar da waka ba tare da hukumar ta tace ba, amma a karshe kotun ta bayar da belinsa tare da dage shari’ar zuwa wani lokaci.
Wannan kame da hukumar ta yi wa Oscar ta janyo cece-kuce a Masana’antar Kannywood inda ’yan fim ke zargin hukumar ta yi haka ne don ramuwar gayya a kan duk dan fim din da bai goyi bayan Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje a zaben da ya gabata ba.
In za a iya tunawa a lokacin yakin zaben bana jaruman Kannywood sun rabu biyu wajen bayar da gudunmawa ga jam’iyyun PDP da APC.
Yanzu haka ana rade-radin cewa hukumar na shirin kama wadansu ’yan fim da ake ganin magoya bayan Jam’iyyar PDP ne, har ana zargin wadansu sun fara kaurace wa sana’ar gaba daya.
Mustapha Naburiska ya shaida wa cewa ya fita daga masana’antar har zuwa lokacin da abubuwa za su gyaru, domin a cewarsa yanzu haka masana’natar ta shiga wani hali da ba zai iya ci gaba da aiki a cikinta ba.
Sai dai a tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano Isma’ila Na’abba Afakallah ya ce, “Babu batun siyasa a cikin wannan lamari domin abubuwa a bayyane suke, wannan darakta ya fitar da waka ba tare da kawo ta gaban hukumarmu don tacewa ba wanda laifi ne da ya saba dokokin hukumar na shekara 2001. Da muka kai kotu kuma ba cewa muka yi ga wani ba ya goyon bayan Gandujiyya ko APC ba. Namu shi ne mu kai kotu cewa muna zargin wane da laifi kaza, kuma kotu ce za ta bincika in ta samu mutum da laifi ta yi masa hukunci idan ba ta samu ba ta sallame shi. Duk abin da aka kai shi gaban kotu shi ne karshen adalci. ”
Game da cewa wakar ta kai shekara biyu da fita ba tare da hukumar ta dauki mataki a kai ba, Afakalalh ya ce “Hukuma tana daukar mataki ne lokacin da abu ya zo gabanta, don waka ta dade da fita ba shi ne yake goge laifin da aka yi ba. Idan misali barawo ya saci mota sai bayan shekara biyu aka gan shi da ita, sai a ce ba za a yi masa hukunci ba? Koda a ce hukuma ta ba mutum takardar shaida fitar da kayansa amma daga baya ta gano abin zai iya zama illa ga jama’a za ta iya kwace takardar shaida ta hana sayarwa.”
Afakallah ya ce, “Ba za mu kyale duk wanda yake so ya shiga rigar siyasa ya ci mutunci da lalata tarbiyyar ’ya’yan al’umma ba. Idan ka san ba ka yi komai ba, to hukumarmu ba za ta samo laifi ta lika maka ba. Amma duk wanda yake son cutar da al’ummar Jihar Kano ko’ina ya shiga ba za mu kyale shi ba. Ba za mu yarda wani ya taso daga wani gari ya zo Kano ya kawo mana abubuwan da ba su yi daidai da mu ba ya dage sai mun bi abin da ake yi a wata jiha. Muna da tsarinmu na nishadantarwa kuma ya zama dole kowa ya bi shi idan zai yi wannan sana’a a Kano. Surutun mutane ba zai hana mu aikinmu ba. A shirye muke mu karbi kowane irin suna matukar a kan kare mutunci da addini da al’adar al’ummar Jihar Kano ne.”
Ya ce babu gwamnatin da ta yi wa Masana’antar Kannywood gata kamar gwamnatin Ganduje ya ce ta tsaya wa ’yan fim a matsayin garanto domin su karbi bashi daga bankuna. Sannan ta fitar da komai yadda za a samar da gidajen kallo na zamani. Kuma ta dauki ’yan fim 450 ta kai su Makaranatar Fim ta Jos ta ba su horo kan abubuwa daban-daban. Kuma ta dauki ’yan fim ta kai su har kasar Moroko don koyo yadda ake tsarin kasuwancin fim a zamanance da yadda ake daukar fina-finai na tarihi. Kuma saboda yadda take son bunkasa masana’antar sai da ta bude ofisoshin hukumarsu a dukkan kananan hukumomin jihar 44.
Afakallah ya ce a yanzu sun sa doka dole masu sutudiyo su rufe da zarar karfe 10 na dare ta yi, domin akwai abubuwan da suke faruwa a wurin. Ba zai yiwu hukuma ta kau da kai don za a zarge ta ko a ce ta yi siyasa ba. Shugaban na Hukumar ya yi kira ga ’yan fim din Hausa da su bi doka a zauna lafiya.