Ba za mu rusa asusun hadin gwiwa da kananan hukumomi ba – Gwamna Sani Bello

A makon jiya Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi jawabin cika kwana 100 a mulki ga al’ummar jihar. Bayan jawabin ne ’yan jarida suka yi masa tambayoyi kan yadda ake gudanar da al’amuran jihar: Me ya zo maka a zuciya lokacin da ka dauki rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga Mayun […]

Ba za mu rusa asusun hadin gwiwa da kananan hukumomi ba – Gwamna Sani Bello
Ba za mu rusa asusun hadin gwiwa da kananan hukumomi ba – Gwamna Sani Bello

A makon jiya Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi jawabin cika kwana 100 a mulki ga al’ummar jihar. Bayan jawabin ne ’yan jarida suka yi masa tambayoyi kan yadda ake gudanar da al’amuran jihar:

Me ya zo maka a zuciya lokacin da ka dauki rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga Mayun bana?
Magana ta gaskiya abubuwa da yawa sun yi ta yi mini sake-sake yayin da na dauki rantsuwar kama aiki. Na yi tsammanin da zarar na shiga ofis zan fara aiki gadan-gadan domin in dora jihar a turbar da ta kamata cikin kankanen lokaci. Da na zauna sai na lura cewa muna da jan aiki a gabanmu, sai na nemo kwararru domin bayar da shawarwarin da suka dace kuma sun yi abin da ya kamata. Ina farin cikin shaida muku cewa mun gano bakin zaren kuma mun fara samun nasarorin da za su sa kwalliya ta biya kudin sabulu. Nan ba da dadewa ba za mu samu karin nasarorin da muka kudurta tun farko.
Yaya za ka kwatanta watannin da ka yi kana jan ragamar jihar?
Shugabanci irin wannan ba abu ne mai sauki ba, dalili shi ne kowa yana bukatar ganawa da Gwamna. Ina da jan aiki a gabana domin in tabbatar da na sauke nauyin da al’ummar jiharmu ta dora min na in yi musu shugabanci nagari. Ina fatan nan ba da dadewa al’amura za su kankama yadda ya kamata.
Ana ce gwamnati na fama da dimbin kalubale sabda karancin kudi, ta wace hanya za ku biya bukatun al’ummarku?
Muna da dimbin kalubale yadda kuka nuna musamman na kudi. Dole mu nemi hanyoyin da za mu shawo kan wannan kalubale da ke gabanmu. Alamu sun nuna cewa ba za mu ci gaba da dogaro da kason da jihar ke samu daga Asusun Tarayya ba. Wajibi ne mu nemi hanyoyin da za mu kaurara nauyin aljihun gwamnatin jiha don jama’a su ci gaba da more mulkin dimukuradiyya, musamman a wannan marrar da guguwar canji ta kada a sassan kasar nan.
Ina kuka samu kudin gudanar da ayyuka daban-daban a jihar alhalin kuna kukan rashin kudi?
Al’amarin gwamnati, al’amari ne na ci gaba. Mun yi la’akari cewa akwai bukatar a ci gaba da ayyukan da muka ga cewa suna da tasiri da amfani ga jama’a ba sai mun kawo wasu daban ba, gwamnatin da ta gabace mu ta bar ayyukan da ba ta kammala ba wasu an kai kashi 60 zuwa 80, za mu ci gaba da gudanar da wadannan ayyuka. Mun rage yawan masu bin mu a duk lokacin da za mu yi tafiya. Mun rage yawan masu yi mana hidima da kudin gudanar da al’amuran gidan gwamnati. Wannan matakin ya taimaka mana wurin samun kudin gudanar da ayyuka masu muhimmanci.
Wadanne hanyoyi kake bi domin jan hankalin masu zuba jari zuwa jihar?
Daga hawanmu mulki mun samu tayi daga masu sha’awar zuba jari daga kasashen waje. Ka san na taba rike mukamin Kwamishina, a lokacin na fahimci wasu daga cikin irin wadannan tayin ba sa haifar da da mai ido. Muna nazarin tayin da suka yi da kuma la’akari da wuraren da suke da sha’awar zuba jari. Ina fata nan da karshen wannan shekarar za mu iya tantance wadanda da gaske suke a wannan fanni na zuba jari.
Mene ne dalilin rage yawan manyan sakatarori da ka yi?
Mun samu manyan sakatarori fiye da 50 da ko Gwamnatin Tarayya ba ta da adadinsu. Kuma babbar matsalar ita ce babu kudi, dole ne mu rage girman gwamnati saboda a samu kudin da za a iya yi wa jama’a aiki, Jihar Neja ba ta da karfin daukar nauyin manyan sakatarori masu yawa haka. Rage yawansu ya zama dole yadda sauran jihohi suka bi sahu kuma suka aikata kowa ya gani.
Me kuka gano dangane da lamarin da ya shafi kudi daga gwamnatin da ka gada?
Maganar kudi akwai abubuwa da yawa a kasa, kuma har yanzu ana kan bincikensu a hankali. Wadanda muka gani a yanzu gaskiya ba mu ji dadinsu ba, lokuta da dama an cire biliyoyin Naira daga asusun gwamnati inda aka yi abin da aka ga dama. Gaskiya akwai babbar matsala tare da wannan al’amari. Tuni muka kafa kwamiti da mambobinsa suka share akalla wata biyu suna ayyukan da muka sa su, suna aikinsu yadda muka tanadar musu tare da ba mu shawarwarin da suka dace.
Ko shakka babu za mu dauki mataki a kan mutanen da suka yi amfani da kudin gwamnati ta hanyar da ba ta kamata ba. Sakamakon binciken da kwamiti ya yi an gano cewa an ba shugabannin Jam’iyyar PDP kudin jama’a domin biyan bukatun kansu. Abin da muke son sani shi ne, ina hujjar daukar kudin gwamnati a ba shugabannin jam’iyya? Kudin gwamnati na jama’a ne baki daya, wadannan suna daga cikin abubuwan da idanunmu suka gane mana. Duk abin da kuka ji mun gaya muku muna da cikakkiyar hujja a kai, muna da sunayen wadanda suka amafana da badakalar. Akwai kudin da aka ciwo bashi aka yi ungulu da kan zabo da su. Su ma duk muna da hujjoji a kai, in mun gama za mu tattara mu ba hukuma ta yi aikinta.
Mene ne matsayin gwamnatinka game da bude asusun gwamnati barkatai?
Jihar Kaduna ita ta fara daukar wannan matakin in da aka shaida mata cewa ana da asusun gwamnati 40, daga baya ta gano sama da 100. Mu ma a nan Neja muna da asusun gwamnati da yawa ana aringizo da kudin gwamnati tare da sama-da-fadi, saboda haka za a rufe duk wani asusun gwamnati a bankuna a bude daya tak. Daga baya, za mu sa kowace ma’aikata ta bude asusu daya, wasu ma’aikatu suna da asusu biyar daban-daban a bankuna, wasu na da 10, wasu 20. Irin wadannan abubuwan suke sa ana tafka barna kuma ba a ganewa da wuri.
Za ku ci gaba da Asusun Hadin Gwiwa na Jiha da kananan Hukumomi?
Za mu ci gaba da wannan Asusun Hadin Gwiwa don yana da kyau da kuma fa’ida, amma sai an yi wa tsari kwaskwarimar da ta kamata. Ko kadan ba za mu so mu ci gaba da lamarin yadda muka same shi ba. Don an yi amfani da asusun an tafka barna fiye da yadda ake tsammani. Idan aka yi masa kwaskwarimar da ta kamata al’umma za ta ji dadin lamarin tare da ganin ayyuka zahiri a kasa musamman a yankunan karkara da akasari ke kananan hukumomi.
Da gaske ne wasu daga cikin wadanda ake zargin sun saci dukiyar jihar sun fara dawowa da ita?
Ba ni da labarin nan, kuma ban gani ba. Ina fata da gaske ne, in da gaske ne za mu yi amfani da kudin mu yi wani aikin da jama’a za su amfana.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi