‘Ba za mu yarda da gwajin maganin coronavirus a Kano ba’

Wata kungiyar farar hula mai suna Kungiyar Matasan Jihar Kano ta soki lamirin gwajin maganin coronavirus da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta yi a jihar Kano bisa sahalewar gwamnati. Kungiyar ta nuna mamakinta game da dalilan da suka sa aka zabi jihar ano don yin gwajin maganin. Idan za a iya tunawa Ministan […]

‘Ba za mu yarda da gwajin maganin coronavirus a Kano ba’

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus (Hoto: France24)

Wata kungiyar farar hula mai suna Kungiyar Matasan Jihar Kano ta soki lamirin gwajin maganin coronavirus da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta yi a jihar Kano bisa sahalewar gwamnati.

Kungiyar ta nuna mamakinta game da dalilan da suka sa aka zabi jihar ano don yin gwajin maganin.

Idan za a iya tunawa Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire ya bayyana cewa WHO za ta yi gwajin maganin a wasu jihohi da suka hada da Kano da ma Yankin Babban Birnin Tarayya bayan amincewar da Najeriya ta yi ta bi sahun kasashen da suka shiga tsarin.

A wata takarda da ya fitar, shugaban Kwamitin Amintattu na kungiyar, Kwamared Haruna Dambatta, ya nuna damuwa game da yadda ake kokarin mayar da jihar sansanin gwajin maganin cutar wadda ta hallaka mutane da dama a fadin duniya.

Kungiyar ta ce ba za ta zuba ido a maimaita abin da aka yi a shekarar 1996 ba – lokacin da kamfanin Pfizer ya yi gwajin maganin Trovan a kan yaran jihar, lamarin da ya janyo rasuwar kimanin yara 12 tare da illata wasu da dama.

Gwajin dai wani yunkuri ne na kasashen duniya a karkashin jagorancin WHO na samar da wani magani da allurar rigakafi cikin gaggawa don kawar da cutar ta COVID-19.

Kasashe 120 ne dai suka amince su shiga a dama da su a lamarin, kuma tuni har an ware mutane 1,500 a wasu kasashe biyar don gudanar da gwajin.

An Ambato shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), Dokta Francis Faduyile, yana cewa ko da yake gwamnati ba ta tuntube su game da gwajin ba, ya san cewa wani mataki ne na kimiyya don tabbatar da ingancin magani ko allurar rigakafi.

Ya kara da cewa wannan gwajin ba ya nufin za a yi amfani da ’yan Najeriya a matsayin zakarun gwajin dafi.