Ba za mu yarda da shisshigin wasu kabilu cikin harkar Fulani ba- Miyetti Allah
kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta zargi wasu daga cikin kabilun kasar nan da yi mata shisshigi cikin al’amuranta, inda ta ce ba za ta lamunci hakan ba. Shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ne ya bayyana hakan a yayin da yake mika lambar yabo ga shugaban kungiyar na Jihar […]
kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta zargi wasu daga cikin kabilun kasar nan da yi mata shisshigi cikin al’amuranta, inda ta ce ba za ta lamunci hakan ba.
Shugaban kungiyar ta kasa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo ne ya bayyana hakan a yayin da yake mika lambar yabo ga shugaban kungiyar na Jihar Nassarawa Alhaji Gidado Idris a lokacin wani biki da ya gudana a ofishin kungiyar na kasa da ke Abuja.
Bodejo ya ce a kwanakin nan sun gano cewa wadansu da ba Fulani ba ne ke haddasa husuma a kungiyar ta hanyar shiga cikin kungiyarsu duk da cewa ba Fulani ba ne.
Ya ce kungiyar ta ba da lambar yabo ne ga Alhaji Gidado Idris saboda kokarinsa na kawo ci gaba mai yawa a cikin kankanen lokaci bayan an zabe shi.
Ya ce Alhaji Gidado ya yi kokari wajen hada kan al’ummar Fulani a Jihar Nasarawa.
A jawabinsa shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Nassarawa Alhaji Gidado Idris ya bayyana farin cikinsa, sannan ya bukaci Fulani su guji jefa kansu cikin rudani musamman a zaben da ke tafe.
A karshe ya ja hankali Fulani kan su zabi jama’a nagari a matakin jihar da kasa baki daya.