Ba za mu yarda sojoji su mulki Nijar tsawon shekara uku ba — ECOWAS

Sanarwar da Janar Tchiani ya fitar dabara ce ta buƙatar tattaunawa.

Ba za mu yarda sojoji su mulki Nijar tsawon shekara uku ba — ECOWAS

ECOWAS

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta ce ba za ta amince sojoji su ci gaba da rike mulkin Nijar ba har nan da shekaru uku masu zuwa.

ECOWAS na wannan batu a matsayin martani da maganar da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi na cewa zai mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuradiyya cikin shekara uku masu zuwa.

Cikin wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya fitar da maraicen ranar Asabar, ya ce zai miƙa mulki hannun farar hula cikin shekara uku.

A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan harkokin siyasa da tsaro da tabbatar zaman lafiya na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa, ya ce yana ganin sanarwar da Janar Tchiani ya fitar dabara ce ta buƙatar tattaunawa.

Ya ƙara da cewa ya kamata a ce jagororin sojin Nijar sun mayar da hankali wajen yaƙar ’yan ta’adda, maimakon harkokin mulkin ƙasar.

Ƙungiyar dai na buƙatar sojojin su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum kan mulki ba tare da ɓata lokaci ba.

ECOWAS ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soji domin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

To sai dai cikin sanarwar da ya fitar, ranar Asabar, Janar Tchiani ya yi gargaɗin cewar amfani da ƙarfin soji ka iya wargaza zaman lafiyar ilahirin yankin Yammacin Afirka.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo