Ba za mu yi karya don kare muradun gwamnati ba — Ministan Labarai
Sai dai ministan ya gargadi ‘yan Najeriya kan yada labaran karya.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Muhammed Idris, ya ce ba zai yi karya don kare gwamnati ba.
Da yake magana a lokacin da ya shiga ofis bayan rantsar da shi, sabon ministan ya ce ma’aikatarsa da gwamnati za su kasance masu gaskiya yayin bayar da bayanai.
- Uba Sani ya rage karin kudin makarantu da El-Rufai ya yi a Kaduna
- ’Yan ta’adda sama da 100 sun mutu a gumurzu tsakanin Boko Haram da ISWAP
Ya ce gwamnati za ta karbi duk inda ta yi kuskure sannan ta yi kokarin daidaita inda ya dace.
Idris ya ce tsarin kasa zai kasance babban al’amari na gwamnati, don haka “nan da kwanaki kadan za mu gabatar da shirye-shiryenmu ga ‘yan Najeriya.”
Ya yi kira ga ‘yan kasar da su guji labaran karya kuma a ko yaushe su fayyace al’amura kafin su kai ga bayyana wa jama’a.
Muhammad Idris ya jaddada cewa ma’aikatar za ta kasance mai bin diddigi da kuma bude kofar gabatar da sahihan bayanai ga ‘yan Najeriya.
A nata bangaren, Ministar Fasaha, Al’adu da Kirkire-Kirkire, Hannatu Musawa, ta ce ma’aikatar za ta daga Najeriya a idon duniya, sannan kuma za ta jajirce wajen samar wa Najeriya kudin shiga.
Ta ce ma’aikatar za ta kuma yi duk abin da za ta yi don sauya munanan labaran da ake yadawa a kan Najeriya a fadin duniya.
Musawa ta kuma bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a dawo da hadin kan kasar nan wanda shi ne burin da suke fata Najeriya ta dore a kai.