Ba za mu yi siyasar ungulu da kan zabo a Ogun ba – ‘Yan Arewa

Al’ummar Arewa mazuna Jihar Ogun sun ce ba za su yi siyasar ungulu da kan zabo ba, saboda tirka-tirkar da jam’iyya mai mulki ta APC ke ciki a jihar. Bangaren Gwamnan Jihar Sanata Ibikunle Amosun yana da ja kan dan takarar Gwamna da jam’iyyar ta tsayar wato Dapo Abiodun lamarin da ya sa  Gwamnan ya […]

Ba za mu yi siyasar ungulu da kan zabo a Ogun ba – ‘Yan Arewa

Al’ummar Arewa mazuna Jihar Ogun sun ce ba za su yi siyasar ungulu da kan zabo ba, saboda tirka-tirkar da jam’iyya mai mulki ta APC ke ciki a jihar. Bangaren Gwamnan Jihar Sanata Ibikunle Amosun yana da ja kan dan takarar Gwamna da jam’iyyar ta tsayar wato Dapo Abiodun lamarin da ya sa  Gwamnan ya yi kira ga magoya bayansa su yi siyasar ungulu da kan zabo, su zabi Shugaba Buhari a sama sannan a matakin jiha su zabi dan takarar Gwamna da ya tsayar Akinlade a wata jam’iyya ta daban.                                                                                     ’Yan Arewa mazauna jihar ta Ogun sun bayanna cewa su ba za a yi irin wannan  tafiyar ba, domin ba su amfana da komai a mulkin Gwamna Amosun ba, sun ce duk da gwagwarmaya da gudunmawarsu a siyasance ba a dauke su da mahinmmanci ba. Sun ce ko a baya sai da aka dauki masu bai wa Gwamna shawarwari da mataimaka na musamman 570, kowace karamar hukumar mutum 10 amma babu dan Arewa ko guda da aka dauka duk da yawan jama’ar Arewa a manyan garuruwan jihar da suka hadar da Abeokuta da Shagamu da Ijebu-Ode da Ifo da sauransu.

Al’ummar Arewar sun bayyana haka ne lokacin da suka ziyarci dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar APC, Cif Dapo Abiodun a gidansa da ke Iperu a Ijebu-Ode a ranar Litinin da ta gabata, inda suka nuna mubaya’arsu gare shi da kuma shigar da bukatunsu.

Alhaji Usman Saffan jagoran kungiyoyin ’yan Arewa mazauna jihar ne ya yi jawabi a madadin ’yan Arewar, inda ya bayyana dalilansu na mara wa dan takarar Jam’iyyar APC baya, a cewarsa ba za su yi siyasar ungulu da kan zabo ba. Don haka ne za su zabi Shugaba Muhammadu Buhari su kuma zabi dan takarar Gwamnan na Jam’iyyar APC domin ya nuna alamun shi na al’umma ne.

A jawabin dan takarar ya nuna farin cikinsa bisa irin goyon bayan da ’yan Arewa suke ba shi, kuma ya ba su tabbacin damawa da su a lokcin yakin neman zabe da kuma bayan an kai ga cimma nasara. Sannan ya ce a wannan karon za a bai wa ’yan Arewar damar shigowa a dama da su a harkokin siyasar jihar.