Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba —Gwamnonin Arewa maso Yamma
Ya buƙaci al’umma su taimaka wajen tona asirin masu bai wa ’yan bindiga bayanan sirri, yana mai cewa yawancin hare-haren da ake kaiwa suna samun goyon bayan wasu daga cikin al’umma.
Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun ɗauki matsayar ƙin yin sulhu da ’yan bindiga, suna masu jaddada cewa dole ne ’yan ta’addan su miƙa wuya ba tare da bayar da wani sharaɗi ba.
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ne ya sanar da cewa gwamnatocin jihohin yankin na zuba kuɗaɗe da ƙarfafa aiki ga jami’an tsaro domin kawo ƙarshen ’yan bindiga da sauran laifuka.
“Ba za mu yi sulhu da masu aikata laifi ba, kuma ba za mu amince da duk wani sharaɗi daga gare su ba, sai dai su miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Katsina yayin ƙaddamar da titin Yanɗaki–Shinkafi–Ƙofar Sauri da gwamnan jihar, Dikko Radda, ya gina.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Lahadi, yana mai buƙaci al’umma su taimaka wajen yaƙi da matsalar ta hanyar tona asirin masu bai wa ’yan bindiga bayanan sirri, yana mai cewa yawancin hare-haren da ake kaiwa suna samun goyon bayan wasu daga cikin al’umma.
“Dole mu kasance masu lura tare da sanya ido kan duk wani motsi na waɗanda ake zargi,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da addu’a domin samun nasarar ƙoƙarin da ake yi na dawo da zaman lafiya.
Ya yaba wa Dikko Raɗɗa kan kafa rundunar tsaro ta Community Watch Corp, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen ƙarfafa tsaron jihar.
A cewarsa, Sakkwato ma ta kafa nata rundunar bayan ganin yadda aka ƙaddamar da irin wannan tsari a jihar Katsina.