Ba za mu yi watsi da binciken mai ba saboda harin boko haram-Farfesa Njodi
Shugaban Jami’ar Maiduguri, Farfesa Ibrahim Njodi, ya ce harin kungiyar boko haram na kwanannan bai zai sanyaya gwiwar jami’ar ba wajen shiga duk wani sako da lungu da jami’an kamfanin mai na NNPC don binciken mai fetur a yankin tafkin kogin Chadi. Njodi ya yi furucin ne a karshen makon da ya gabata yayin da […]

Shugaban Jami’ar Maiduguri, Farfesa Ibrahim Njodi, ya ce harin kungiyar boko haram na kwanannan bai zai sanyaya gwiwar jami’ar ba wajen shiga duk wani sako da lungu da jami’an kamfanin mai na NNPC don binciken mai fetur a yankin tafkin kogin Chadi.
Njodi ya yi furucin ne a karshen makon da ya gabata yayin da yake karbar tawagar Karamin Ministan Mai da Albarkatun Kasa, Dokta Ibe Kachikwu.