‘Ba za mu zama ’yan amshin shata ga bangaren zartarwa a Yobe ba’
Shugaban Majalisar Dokokin ta Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya ce wakilan majalisar ba za su zama ’yan amshin shata ga bangaren zartarwa na jihar ba, sai dai za su ci gaba da hada hannu don ciyar da jihar gaba. Alhaji Adamu Dala Dogo ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema […]
Shugaban Majalisar Dokokin ta Jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya ce wakilan majalisar ba za su zama ’yan amshin shata ga bangaren zartarwa na jihar ba, sai dai za su ci gaba da hada hannu don ciyar da jihar gaba.
Alhaji Adamu Dala Dogo ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan da kaddamar da sabuwar majalisar a ranar Litinin a garin Damaturu.
Shugaban majalisar ya ce, majalisarsu tana tsaye kan kafafunta wajen sauke nauyin da ke
kanta na yin dokokin da suka dace da al’umma za su amfana ba tare da yarda wani ya yi amfani da su ba, balle su zama ’yan amshin shata kamar yadda ’yan adawa ke zarginsu.
Ya gode wa mambobin majalisar kan sake zabarsa a matsayin shugaban majalisar a karo na biyu
inda ya ba su tabbacin zai ci gaba da jagorantarsu bisa adalci, kuma ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ’yan majalisar za su ci gaba da samar da muhimman kudirorin da za su ciyar da jihar gaba.
Ya gode wa Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam kan yadda shi da bangaren zartarwa suke ba su goyon baya wajen gudanar da ayyukansu.